Matashi Ya Kulle Mahaifansa A Daki, Ya Saci Motarsu Da Wasu Kayayyaki A Jihar Ogun

Matashi Ya Kulle Mahaifansa A Daki, Ya Saci Motarsu Da Wasu Kayayyaki A Jihar Ogun

  • Dubun wani matashi ya cika bayan ya kulle mahaifansa tare da musu mummunan sata
  • Wanda ake zargin mai suna Ayomiposi Esan dan shekaru 17 ya saci wayoyin salula 3 da janareta 2 da wata mota a jihar Ogun
  • Sai dai iyayen yaron bayan an kama shi sun bukaci a sake shi ba tare da daukar mataki a kansa ba

Jihar Ogun - Wani matashi mai shekaru 17 ya fakaici iyayensa tare da tafka musu mummunan sata a jihar Ogun.

Matashin mai suna Ayomiposi Esan ya sace wayoyin salula 3 da janareta 2 da kuma mota kirar Toyota Corolla, Legit.ng ta tattaro.

'Yan sanda sun kama kan satar motar iyayensa
Rundunar 'yan sanda ta kama matashi kan zargin satar motar iyayensa. Hoto: OgunPoliceNG.
Asali: Facebook

Meye matashin ya sata a Ogun?

Esan ya samu nasarar yin satar ne bayan ya kulle mahaifan nasa da kwado a daki a Ogiji da ke karamar hukumar Sagamu a jihar.

Kara karanta wannan

“Kada Ku Kuskura Ku Bar Matayenku Ku Tafi Turai”: Dan Najeriya Da Ke Zaune a UK Ya Gargadi Ma’aurata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Punch ta tattaro cewa matashin a ranar 3 ga watan Satumba ya kutsa kai cikin gidan inda ya samu iyayen nasa na bacci da tsakar dare.

Wata majiya ta bayyana cewa da kyar aka samu aka ceto iyayen daga dakin bayan yaron ya tsere da kayayyakin.

Bayan kai rahoto ga 'yan sanda, rundunar ta yi nasarar cafke shi a jihar Legas ya na kokarin siyar da kayan.

Majiyar ta ce:

"Matashin ya riga ya siyar da janareta guda daya, iyayen ba sa son a hukunta yaron nasu.
"Jami'an 'yan sanda na son hukunta yaron amma iyayen sun bukaci a sake shi da kayayyakin da ya sata."

'Yan sanda sun kama matashi kan sata

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Omotola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ta ce rundunarsu ta so ta dauki matakin hukunci a kan yaron amma iyayensa ba sa bukatar hakan, Head Topics ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ya za a yi? Davido ya ce kudi ne matsalar Najeriya, ya ba da shawarin mafita

Ta ce:

"Mahaifan yaron sun kawo cikas a binciken da mu ke saboda ba sa son a hukunta shi.
"Mun bai wa yaron shawara ya sauya halayensa don zama mutum na gari a cikin al'umma.

Matashi Ya Hallaka Mahaifinsa Kan Abin Duniya

A wani labarin, wani matashi ya hallaka mahaifinsa don yin tsafi da neman kudi a jihar Ogun.

Tuni jami'an 'yan sanda su ka kama matashin tare da fara bincike na musamman a kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel