Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kaddamar da Shirin Tsaftace Jihar Kano Daga Shara da Datti

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kaddamar da Shirin Tsaftace Jihar Kano Daga Shara da Datti

  • Gwamnatin jihar Kano ta dauki matasa 4500 aiki don tsaftace tituna a jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Hakan zai rage yadda shara da datti ke yaduwa a jihar, kamar yadda rahoton da muka samo ya bayyana
  • Hakazalika, ana shirin kawo tsarin sauya shara ta zama takin zamani a jihar Kano, inji gwamna Abba Kabir Yusuf

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dauki matasa 4,500 aiki a matsayin masu sharar titi domin tsaftace birni.

An kaddamar da shirin kiyaye tsaftar jihar Kano mai taken "Operation Nazafah" ne a fadar mai martaba Sarkin Kofar Kwaru.

Hakan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Malam Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a ranar Lahadi, a jihar, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Ɗalibar Jami'ar Tarayya Ta Mutu a Hanyar Zuwa Kasuwa

Abba Gida-Gida ya dauki aikin sharar titi a Kano
Gwamnan Kano ya dauki masu shara aiki a Kano | Hoto:Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Dawakin-Tofa ya ce gwamnatin jihar ta sayi karin manyan motoci 10 domin aikin tattara sharar a fadin jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matasan da za su yi aikin shara

Hakazalika, ya sanar da daukar matasa 4,500 aiki don yin sharar a kullun a karkashin hukumar kula da tsaftar muhalli ta REMASAB don share dukkan manyan titunan birnin, Platinum Post ta tattaro.

A cewar wani yanki na sanarwar:

“Baya ga karin manyan motoci guda 10, mun kuma sayo na karin masu daukar nauyi guda biyu da kuma gyara wasu manyan injuna da manyan motoci da dama domin gudanar da aikin."

Kiran gwamna ga wadanda aka dauka aiki

Gwamnan, ya bukaci wadanda aka dauka aikin da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu domin cimma burin da ake so na tsaftace gari da samar da koshin lafiya ga kowa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Koka, Ya Ce 'Yan Bindiga Sun Mamaye Jiharsa

Gwamnan ya kuma bayyana cewa nan ba da dadewa ba gwamnatin jihar za ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna don sarrafa shara zuwa takin zamani.

A cewarsa, hakan zai samar da karin guraben ayyukan yi, kudaden shiga ga gwamnati da kuma inganta muhallin lafiya ga mazauna birnin.

Yadda shara ta toshe titi a Kano

A wani labarin, titin Court Road da ke cikin birnin Kano, ya cike da tarin shara wacce ta mamaye shi ta yadda masu ababen hawa basa iya bi ta kansa.

Titin wanda yake a yankin Sabongari, ya kasance daya daga cikin hanyoyin da a ke bi wajen shiga kasuwar Yankura dake cikin birnin na Dabo.

Wasu daga cikin ‘yan kasuwar da ke hada-hada a yankin, sun koka kan barazan kamuwa da cututtuka sakamakon sharar da aka jibge a kan titin. Sun bayyana hakan ne a zantawarsu da jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Wike Ya Yi Babban Albishir Ga Yan Najeriya Kan Gwamnatin Tinubu, Ya Ce Romon Dadi Na Nan Tafe

Asali: Legit.ng

Online view pixel