Kotun Zabe Ta Tanadi hukuncinta Kan Shari'ar Gwamnan Jihar Kano

Kotun Zabe Ta Tanadi hukuncinta Kan Shari'ar Gwamnan Jihar Kano

  • Kotu ta ɗage sauraron ƙarar zaɓen gwamnan jihar Kano, tsakanin Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan Kano ta ɗage sauraron ƙarar ne bayan jam'iyyun APC da NNPP sun kammala bayanansu na ƙarshe a gaban kotun
  • A halin da ake ciki, kotun ta tanadi hukuncinta a kan ƙarar da ke ƙalubalantar nasarar Abba Kabir, inda ta ce za ta sanar da hukuncinta nan bada daɗewa ba

Jihar Kano - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kano ta tanadi hukuncinta a kan ƙarar da ke ƙalubalantar nasarar, gwamna Abba Kabir Yusuf a zaɓen gwamnan jihar.

Kotun sauraron ƙarar ta sanar da hakan ne a ranar Litinin, 21 ga watan Agustan 2023.

Kotu ta shirya yanke hukunci kan shari'ar gwamnan Kano
Kotun zaben ta tanadi hukuncinta kan karar Gawuna da Abba Hoto: @AbubakarmusaDK1, @Kyusufabba
Asali: Twitter

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta shigar da ƙarar ne domin ƙalubalantar nasarar Abba Kabir Yusuf, na jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), ta Rabiu Musa Kwankwaso, a zaɓen gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: An Bankado Wani Sabon Tuggu Da Tinubu Ke Shiryawa a Kan Atiku Abubakar

Shugabar kotun mai alƙalai uku, mai shari'a Oluyemi Akintan-Osadebay, wacce a madadin sauran alƙalin ta yi alƙawarin yin adalci, ta ce hukuncin kotun zai zo ƙasa da kwanaki 180 da doka ta tanada, cewar rahoton Daily Trust.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kotu ta dage sauraron ƙarar kan nasarar Abba

An ɗage sauraron ƙarar ne bayan dukkanin ɓangarorin biyu sun kammala gabatar da bayanansu a gaban kotun, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Jam'iyyar APC ta buƙaci kotun da ta tabbatar da ƙorafinta tare da sanar da Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen, yayin da hukumar INEC, jam'iyyar NNPP da Abba Kabir suka buƙaci kotun da ta yi fatali da ƙarar.

Tun da farko dai masu zanga-zanga sun fito kan titunan birnin Kano kan shari'ar, duk da umarnin da kwamishinan ƴan sandan jihar ya bayar na hana kowace irin zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Abdourahmane Tchiani Ya Fadi Matakin Da Za Su Dauka Idan ECOWAS Ta Kawowa Nijar Hari

Kotu Ta Tanadi Hukunci Kan Shari'ar Gwamnan Ebonyi

A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Ebonyi, ta tanadi hukuncinta kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar.

Jam'iyyun Peoples Democratic Party (PDP) da APGA na neman a soke nasarar gwamna Francis Nwifuru na jam'iyyar APC, saboda ba halastaccen ɗan jam'iyyar ba ne a lokacin da a ka yi zaɓen gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng