“‘Yan Bindiga Sun Mamaye Mu”, Gwamnan Bauchi Ya Koka

“‘Yan Bindiga Sun Mamaye Mu”, Gwamnan Bauchi Ya Koka

  • Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya koka kan ayyukan 'yan bindia a jiharsa
  • Gwamnan ya ce yan bindigar da ake fatattaka daga sauran yankunan kasar suna shigowa jihar Bauchi don samun mabuya
  • Ya roki gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu da ta kawo masu dauki domin miyagun sun fara kawo karan tsaye ga zaman lafiyar jihar

Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya koka kan ayyukan 'yan bindiga a jihar inda ya ce sun fara shan kansu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa yayin da ya karbi bakuncin sarakunan jihar Bauchi wadanda suka kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati a ranar Asabar, 14 ga watan Satumba, jaridar Punch ta rahoto.

Gwamnan Bauchi ya roki gwamnatin tarayya ta kawo masu dauki kan ayyukan yan bindiga
“‘Yan Bindiga Sun Mamaye Mu”, Gwamnan Bauchi Ya Koka Hoto: Nigerian Tribune
Asali: UGC

'Yan bindiga na shigowa Bauchi daga sauran yankuna, gwamna

Kara karanta wannan

Wike Ya Yi Babban Albishir Ga Yan Najeriya Kan Gwamnatin Tinubu, Ya Ce Romon Dadi Na Nan Tafe

Ya bayyana cewa saboda yaki da gwamnatin tarayya ke yi da yan bindiga da yan ta'adda a sauran yankunan kasar, jihar ta zama mabuyar marasa kishin kasa wadanda suka fara kawo karan tsaye ga zaman lafiyar jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta yi kasa a gwiwa ba tana aiki tukuru don tabbatar da ganin cewa an samu zaman lafiya na rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar, rahoton Politics Nigeria.

Wani bangare na jawabinsa na cewa:

"Dangane da harkokin tsaron cikin gida, ina mai farin cikin sanar da ku cewa mun kafa ma’aikatar tsaron cikin gida da za ta hada gwiwa da gwamnatin tarayya domin kula da batun samar da tsaron cikin gida. Muna da namu ‘yan bangar da ke aiki tare da tsaro da aka kafa.
"Sauran jihohi na kan gaba, muna da mafi yawan al'umma a yankin, saboda haka da ayyukan gwamnatin tarayya a sauran yankuna, yan bindigar na shigowa Bauchi.

Kara karanta wannan

Mun gode: Tinubu ya ba Inyamurai mukamai masu kyau duk da ba su zabe shi ba, Soludo

"Dole sai mun kara kaimi don shan kansu. Muna aikata hakan amma shakka babu, suna kara mamaye mu kuma wannan ne dalilin da yasa muke kira ga gwamnatin tarayya da ta taimake mu sannan ta kawo mana agaji, mu yi abubuwan da suke yi a arewa maso yamma don mu ci gaba da kasancewa a matsayinmu na masu zaman lafiya.
"Sarkin Katagum wani sarki ne da aka sanu da yawan fita fatrol din dare. Ina so sauran sarakuna su yi koyi da shi sannan su yi abun da yake yi, ba wai ba sa yi bane, amma ba kasafai kuke yi ba a naku bangaren."

Ka taimaka a kawo mana agaji, gwamnan Bauchi ya roki Tinubu

Gwamnan ya kuma yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da kada ya yi watsi da jihar Bauchi saboda jiha ce da jam'iyyar adawa ta People’s Democratic Party ce ke shugabanci a cikinta kamar yadda ya koka cewa gwamnatin tarayya ta yi watsi da hanyar jirgin kasa na farko a kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Zai Fara Kama Yaran Da Aka Gani Suna Yawo a Titi a Lokacin Makaranta

Bauchi: Sarkin Ningi ya yi barazanar tsige Sarakunan da ke taimakon yan bindiga

A wani labarin, mun ji cewa Sarkin Ningi a jihar Bauchi a Arewa maso Gabas, Alhaji Yunusa Muhammadu Danyaya, ya gargaɗi dukkan masu riƙe da Sarauta a karakashin masarautarsa.

A rahoton Daily Trust, Sarkin ya yi barazanar tuge rawanin duk wani Hakimi ko mai Anguwan da ya gano yana da hannu a ayyukan 'yan bindigan daji a yankin da yake jagoranta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel