Akwai Aiki a Gaban NNPP a Kano, APC Za Ta Karbe Nasarar Abba a Zaben Gwamnan 2023

Akwai Aiki a Gaban NNPP a Kano, APC Za Ta Karbe Nasarar Abba a Zaben Gwamnan 2023

  • Akwai sauran yaki a Kano domin Jam’iyyar APC ta reshen Jihar za ta shigar da kara a gaban kotu
  • Kakakin APC na Kano, Ahmad Aruwa ya ce za su kalubalanci zaben Shugaban kasa da Jiha na 2023
  • Jawabin Aruwa ya nuna babu ruwan Jam’iyyar APC da jawabin da Nasiru Yusuf Gawuna ya fitar

Kano - Jam’iyyar APC ta reshen Jihar Kano ta nuna za tayi shari’a da Hukumar INEC da jam’iyyar NNPP a kan zabukan da aka gudanar a bana.

Leadership ta kawo rahoto cewa Mai magana da yawun bakin jam’iyyar APC a Kano, Ahmad Aruwa ya fitar da jawabi cewa za su je kotun korafi

Ahmad Aruwa ya ce jam’iyya mai-ci ta dauki wannan matsaya bayan wani taro da aka yi, sai suka ga bukatar su nemi hakkinsu a kotun zabe.

Kara karanta wannan

"An Hada-Kai da INEC, Za a Murde Zaben Gwamna a Jihar Adamawa" Inji Jam’iyyar PDP

Kafin a kai ga wannan matsaya, APC mai mulki a Kano da Najeriya ta bukaci hukumar INEC ta sake nazarin zaben Gwamna da ta shirya.

Ba ayi nazarin zaben Gwamna ba

Har lokaci ya wuce, hukumar zabe ta kasa ba ta duba sakamakon zaben ba, jam’iyyar APC ta na ikirarin zaben da NNPP ta lashe bai kammalu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta so abin da ya faru a zaben Gwamnonin jihohin Adamawa da Kebbi ya faru a Kano bisa zargin cewa an soke kuri’u masu yawan gaske.

Gwamnan Kano
Zababben Gwamnan Kano Hoto: salisuyahayahototo
Asali: Facebook

A cewar jam’iyyar ta APC, tazarar Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna a zaben bai kai adadin kuri’un da INEC ta soke a zaben na Maris ba.

Ganin Abba Kabir Yusuf da Aminu Abdulsalam Gwarzo sun karbi takardar shaidar lashe zaben Gwamna, APC ta tabbatar da za ta shigar da kara.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC ta Kunshe Biliyoyin Kudi Wajen Saida Fam Ga Masu Sha’awar Takara

Rahotanni na cewa uwar jam’iyyar ta nesanta kan ta da ‘dan takararta, Nasiru Yusuf Gawuna wanda ya nuna ya rungumi kaddarar Ubangiji SWT.

Jam’iyyar APC ta ce ba da yawun ta Nasiru Gawuna ya yi wannan magana ba, ta sha alwashin sai an karbe nasarar da NNPP ta samu idan aka je kotu.

Zanga-zanga a Amurka

Rahoto ya zo mana cewa ana zargin ‘dan takaran shugaban kasan LP a zaben 2023, Peter Obi ya shirya ayi zanga-zanga a babban birnin kasar Amurka.

Shugaban jam’iyyar APC na Amurka ya ce gwamnati ba ta goyon zanga-zangar da za ayi a Washington, ya ce Asiwaju Bola Tinubu zai dare mulki a Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel