Abun Kunya: Malami Ya Dirka Wa Matar Abokinsa Ciki a Jihar Ondo

Abun Kunya: Malami Ya Dirka Wa Matar Abokinsa Ciki a Jihar Ondo

  • Mutane sun sha mamaki yayin da wani Malamin Coci ya ɗirka wa matar abokinsa ciki har ta haihu a jihar Ondo
  • Rahoto ya nuna cewa maƙotan mutumin sun yi kokarin ankarar da shi amma ya nuna bai damu ba ko ƙaɗan
  • Daga karshe wasu majiyoyi sun bayyana cewa Malamin, wanda abokin ne ya ba shi wurin zama, ya ɗauke matar daga gidan aurenta

Ondo - Maƙota da iyalai sun shiga tsananin mamaki yayin wani mutumi mai suna Tubosun ya yi zargin cewa matarsa ta haifi cikin da abokinsa tun na yarinta ya ɗirka mata a jihar Ondo.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa matar, wacce ta haifi yara uku tare da Tubosun tun bayan aurensu, ta ƙara haihuwa amma wannan karon ɗan na abokinsa ne wani Malamin Coci.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Ministan Tinubu Ya Gana da Tsohon Shugaban Ƙasa Kan Muhimmin Batu, Bayanai Sun Fito

Malami ya yi wa matar abokinsa na yarinta ciki har ta haihu a Ondo.
Abun Kunya: Malami Ya Dirka Wa Matar Abokinsa Ciki a Jihar Ondo Hoto: thenation
Asali: UGC

Asirinsu ya fasu ne yayin da yayan magidancin, Moses Akinnuoy, ya kai ƙarar Malamin mai suna, Fasto Oluwaseun Akinnubi, kan abubuwan da yake yi a gidansu da ke layin a ƙaramar hukumar Odigbo, jihar Ondo.

Fasto Akinnubi ya maida Falon gidan abokinsa (Mijin matar) zuwa coci inda ya ke gudanar da hidimar ceto ga mutane mabiya addinin Kirista da sunan gidauniyar Kiristoci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda magidanci ya ba Malamin wurin zama

Rahoto ya nuna tun asali mijin matar ne ya ɗauko Malamin cocin ya ba shi matsuguni a gidansu saboda lokacin ya rasa wurin zama.

Majiyoyi sun bayyana cewa lokacin zamansa da ma'auratan ne ya lallaɓa ya ɗirka wa matar abokin nasa wanda ya ba shi wurin zama, ciki.

Wasu bayanai sun nuna cewa Malamin ya taɓa faɗa wa abokinsa cewa Allah ya tsara cewa matar zata zama matarsa, kamar yadda rahotanni suka tattaro.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Tarayya Ya Samu Babban Saɓani da Gwamnan APC Kan Abu 1? Gaskiya Ta Bayyana

Wata majiya ta ce:

"Bayan ya yi wa matar ciki, sai ya kama hayar wani gida kuma ya ɗauke matar daga gidan mijinta ta koma inda yake zama."
"Abun takaicin da maƙotan suka gani shi ne, bayan Mama Precious ta haifa wa faston ɗa, sai aka ga mijin yana zuwa gidan Faston yana wanke kayan matarsa da na jaririn."
"Ɗaya daga cikin makotan ya kira mutumin ya ankarar da shi cewa Malamin ya kwace masa mata, amma ya nuna bai damu ba, daga nan suka gane ba ya cikin hankalinsa."

Hatsarin Babbar Mota da Bas Ya Lakume Rayukan Mutum 5 a Anambra

A wani rahoton na daban kuma Wani mummunan hatsari ya yi ajalin fasinjojin motar bas mata 5 a jihar Anambra, wasu da dama sun ji raunuka.

Ganau sun bayyana cewa kwantenar da wata babbar mota ta ɗauko ce ta faɗa kan Bas ɗin, ta murkushe mutanen a babban titin Awka.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Malamin Da Ya Damfari Wata Baiwar Allah Kuɗi Sama da Naira Miliyan 1.6

Asali: Legit.ng

Online view pixel