An Kama Fasto Bisa Zargin Dambarar Wata Mata Naira Miliyan 1.6 a Jihar Ondo

An Kama Fasto Bisa Zargin Dambarar Wata Mata Naira Miliyan 1.6 a Jihar Ondo

  • Jami'an tsaron rundunar NSCDC sun damƙe wani Malamin addini bisa zargin zambatar wata mata kuɗi N1.67m a jihar Ondo
  • Kakakin hukumar ya bayyana cewa Faston ya damfari wasu mutane da dama da ba a san yawansu ba a lokuta daban-daban
  • Malamin cocin ya karɓi makudan kuɗin daga hannun matar da sunan zai taimaka mata ta sami biza cikin sauƙi

Jihar Ondo - Jami’an hukumar tsaron Sibil Difens ta Najeriya (NSCDC) sun kama wani malamin coci mai suna, Fasto Micheal Ogundepo, mai shekaru 39 a jihar Ondo bisa laifin zamba.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ana zargin Malamin cocin, Ogundepo ya damfari wata wata mai suna, Misis Fagbuyiro Ajetomobi kudi har Naira miliyan 1.6.

An kama Malamin Coci bisa laifin zamba cikin aminci.
An Kama Fasto Bisa Zargin Dambarar Wani Bawan Allah Naira Miliyan 1.6 a Ondo Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Kakakin hukumar NSCDC reshen jihar, Daniel Aidamenbor ya tabbatar da kama wanda ake zargin a wata sanarwa da ya fitar a Akure, babban birnin jihar Edo.

Kara karanta wannan

Al’ummar Yarbawa Sun Yi Wa Kwankwaso Da Gwamnatin Kano Addu’a Ta Musamman

Aidemenbor ya ce malamin da ake zargin ya kwace fasfo din Misis Ajetomobi kuma ya ci gaba da harkokin gabansa da kuɗinta wanda hakan ya hana ta sake neman wata takardar bizar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A jawabinsa, kakakin NSCDC ya ce:

"Mun kama Micheal Ogundepo, ɗan kimanin shekara 39, malamin coci mai lamba 15 a layin Ewu Agbo, Ikorodu Lagos bisa zargin damfarar Misis Fagbuyiro Ajetomobi Yemi da ke zaune a Akure."
"Faston ya zambaci matar ne da sunan zai taimaka mata ta samu Biza a kuɗi N1,670,000. Hukumar mu ta gayyaci wanda ake zargin amma ya ƙi amsa gayyata."
"Ya yi iƙirarin baya ƙasar nan kuma ya yi amfani da lambar ƙasar wajen ta ƙarya wajen kiran matar yana shirga mata ƙarya."
“An kama wanda ake zargin ne lokacin da aka gayyace shi ya karbi kudi N3,000,000 na aikin biza, ba tare da ya san cewa tarko aka ɗana masa ba."

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Ministan Tinubu Ya Tsoma Baki a Rigimar Jam'iyyar APC Da Korar Jiga-Jigai 84

Aidamenbor ya bayyana cewa binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya damfari wasu abokan huldarsa da yawa waɗanda ba a san adadinsu ba, Vanguard ta rahoto.

Sanata Kalu Ya Lallasa Jam'iyyar PDP da Labour Party a Kotun Zabe

Rahoto ya nuna cewa Sanata Kalu na jam'iyyar APC ya samu nasara kan PDP da Labour Party yayin da Kotun zaɓe ta yanke hukunci ranar Talata.

Kotun zaben NASS ta tabbatar da nasarar tsohon gwamnan jihar Abia a matsayin halastaccen sanatan Abia ta arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262