Hatsarin Babbar Mota da Bas Ya Lakume Rayukan Mutum 5 a Anambra

Hatsarin Babbar Mota da Bas Ya Lakume Rayukan Mutum 5 a Anambra

  • Wani mummunan hatsari ya yi ajalin fasinjojin motar bas mata 5 a jihar Anambra, wasu da dama sun ji raunuka
  • Ganau sun bayyana cewa kwantenar da wata babbar mota ta ɗauko ce ta faɗa kan Bas ɗin, ta murkushe mutanen a babban titin Awka
  • Hukumar kiyaye haɗurra (FRSC) ta bayyana cewa tuni jami'ai suka ɗauke gawarwakin kuma suka kai majinyatan asibiti

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Anambra - Wani mummunan hatsari ya rutsa da motar bas ta haya kirar L300 da kuma babbar motar dakon kaya 'Leyland' a mahadar Odumudu da ke kan babban titin Nteje-Awka, jihar Anambra.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa hatsarin ya lakume rayukan fasinjoji biyar yayin da wasu biyar kuma suka samu raunuka daban-daban.

Motoci biyu sun yi hatsari a jihar Anambra.
Hatsarin Babbar Mota da Bas Ya Lakume Rayukan Mutum 5 a Anambra Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Hadarin wanda ya auƙu da misalin karfe 7:30 na safiyar ranar Juma’a ya rutsa da mutane 10, maza uku da mata bakwai.

Kara karanta wannan

"Abinda Ya Sa Iyaye Suka Daina Tura 'Ya'yansu Makarantu a Najeriya" Ministan Tinubu Ya Magantu

Yadda hatsarin ya auku

A cewar wani ganau da abun ya faru a gabansa, lalacewar wani ɓangare na titin ne ya haddasa hatsarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen da ke wurin sun ce motocin biyu sun taho ne daga bangarori daban-daban, amma da suka isa wuri mara kyau a titin, sai kwantenan da ke makale da babar motar ta faɗa kan bas din tare da murkushe wasu daga cikin fasinjoji.

Da take tabbatarwa, muƙaddashin kakakin hukumar kiyaye haɗurra ta Anambara (FRSC), RC Margaret Onabe, ta ce mutum biyar suka mutu yayin da wasu biyar suka ji raunuka.

A cewarta, jami'an sashin ceto na hukumar FRSC daga RS5.33 da ke Nteje sun kai waɗanda suka jikkata zuwa asibitin Divine Care, Umunya domin kula da lafiyarsu.

Haka zalika sun ɗauki gawarwakin waɗanda Allah ya yi wa rasuwa zuwa Asibitin Chira domin kwararrun likitoci su tabbatar da mutuwarsu kafin daga bisani su kai su ɗakin aje gawa na Nteje.

Kara karanta wannan

Hatsarin Kwale-Kwale a Neja: Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Karu Zuwa 30, NSEMA

A halin yanzu da muke kawo muku wannan rahoto, Kwamandan sashin ceto tare da hadin gwiwar Kwamandan Nteje, na kokarin kawar da cikas din da hadarin ya haifar.

Duka waɗanda suka mutu mata ne - FRSC

Shugaban FRSC na jihar Anambra, Adeoye Irelewuyi, ya jajantawa iyalan mamatan. Ya kuma yi fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.

The Nation ta rahoto Shugaban FRSC na cewa:

"Mutane 10 da suka hada da maza 3 da mata 7 ne hatsarin ya rutsa da su, mata biyar daga ciki suka rasa rayukansu."

Adeoye ya bukaci masu ababen hawa da su yi tuki cikin taka tsantsan, kuma su kula da yanayin tituna yayin da suke tafiya.

Innalillahi, Bene Mai Hawa 20 Ya Rushe Kan Jama'a a Babban Birnin Jihar PDP

A wani rahoton na daban Mutane da dama sun samu raunuka yayin da wani gini mai hawa 20 ya kife a Asaba jihar Delta da yammacin Alhamis.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kuma Kai Mummunan Farmaki Da Tsakar Dare, Sun Yi Ajalin Mutane 11, 'Yan Sanda Sun Yi Martani

Ginin otal ɗin na biliyoyin Naira da ke daura da Delta Mall ya ruguje ne da yammacin ranar Alhamis yayin da ma'aikata ke tsaka da aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262