Abbas: Kakakin Majalisar Tarayya Na Rigima da Gwamna Uzodinma? Gaskiya Ta Fito

Abbas: Kakakin Majalisar Tarayya Na Rigima da Gwamna Uzodinma? Gaskiya Ta Fito

  • Abbas Tajudeen ya musanta rahoton da ke yawo a kafafen watsa labarai cewa alaƙarsa ta yi tsami da gwamnan jihar Imo
  • Kakakin majalisar wakilan ya bayyana cewa labarin ƙagagge ne wanda wasu masu ƙulla sharri suka ƙirƙira da wata manufa
  • Ya ce har yanzu yana da alaƙa mai kyau tsakaninsa da gwamna Hope Uzodinma kuma babu wani abu da ya shiga tsakaninsu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Kakakin majalisar wakilan tarayya, Abbas Tajudden, ya musanta raɗe-raɗin cewa shi da gwamnan Imo, Hope Uzodinma, sun samu saɓani, Daily Trust ta rahoto.

Abbas ya ƙaryata rahoton, wanda wasu kafafen watsa labarai suka buga, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Musa Abdullahi Krishi, ya fitar yau Laraba.

Kakakin majalisar wakilan tarayya, Abbas Tajudeen.
Abbas: Kakakin Majalisar Tarayya Na Rigima da Gwamna Uzodinma? Gaskiya Ta Fito Hoto: Abbas Tajudeen
Asali: Facebook

Kakakin majalisar ya ce rahoton mai taken, "Uzodinma ya kai ƙarar Abbas wurin Tinubu saboda ya bai wa Ugochinyere kwamiti mai gwaɓi," bai da tushe balle makama.

Kara karanta wannan

Hadimai 2 Na Gwamnan PDP da Wasu Manyan Jiga-Jigai Sun Koma APC Ana Dab Da Sabon Zaɓe

Rahoton wanda jaridar Leadership ta tattara ya nuna cewa alaƙa ta yu tsami tsakanin Abbas da gwamna Uzodinma

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Menene gaskiyar lamarin?

Da yake musanta labarin, Abbas, ya ce yana da kyakkyawar alaka da Gwamnan Jihar Imo kuma babu wata baraka da ta shiga tsakaninsu kan batun naɗa Ugochinyere, shugaban kwamiti a majalisa.

Shugaban majalisar ya bayyana rahoton a matsayin "kagaggen labari" na sharri da wasu suka ƙirƙira, sannan ya bukaci jama'a da su yi watsi da shi.

Wani sashin sanarwan ya ce:

"An ja hankalin kakakin majalisar wakilan tarayya, Honorabul Abbas Tajudden (Ph. D) kan labarin da wata jarida ta wallafa mai ɗauke da kanun da ke sama kuma yana ta yaɗuwa."
"Kakakin majalisa na sanar da al'umma cewa babu lokacin da gwamna Hope Uzodinma na Imo ya nemi kada a naɗa Honorabul Ikenga Ugochinyere a matsayin shugaban kwamitin albarkatun man fetur."

Kara karanta wannan

Kashim Shettima Ya Bayyana Yankunan Da Za Su Ci Gajiyar Mulkin Shugaba Tinubu

"Abbas Tajudeen yana da kyakkyawar alaka da Gwamna Hope Uzodinma kuma babu abin da ya faru da ya tabbatar da tsamin dangantaka a tsakaninsu.”

Majalisar Dokokin Ogun Ta Karbi Sunayen Kwamishinoni 10 da Gwamna Ya Nada

A wani rahoton na daban Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya tura ƙarin sunayen mutum 10 da ya naɗa kwamishinoni zuwa majalisar dokoki.

Majalisar ta tabbatar da zuwan sunayen, kuma ta fara shirye-shiryen fara tantance su ranar Laraba, 13 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel