Ministan Tinubu Ya Gana da Tsohon Shugaban Kasa Jonathan da Asari Dokubo

Ministan Tinubu Ya Gana da Tsohon Shugaban Kasa Jonathan da Asari Dokubo

  • Abubakar Momoh Ministan raya Neja Delta ya gana da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan kan muhimman batutuwa a Abuja
  • Wata sanarwa daga Ofishin ministan ta bayyana abubuwan da suka tattauna domin kawo ci gaba da yankin mai dumbin arziƙin man fetur
  • Ministan ya kuma gana da Asari Dokubo a yunkurinsa na kawo karshen satar ɗanyen mai da gina Neja Delta

FCT Abuja - Ministan harkokin raya Neja Delta, Abubakar Momoh, ya gana da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, domin tattauna batutuwan da suka shafi yankin Neja Delta.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa daga cikin abubuwan da suka tattauna harda batun yadda za a kawo ƙarshen satar ɗanyen mai da kuma lalata kayan gwamnati.

Ministan Neja Delta, Abubakar Momoh tare da Jonathan da Asari Dokubo.
Ministan Tinubu Ya Gana da Tsohon Shugaban Kasa Jonathan da Asari Dokubo Hoto: Thenation
Asali: UGC

Ministan ya kuma gana da Asari-Dakubo a wani bangare na tuntuɓa da lalubo dabarun samar da mafita ga dimbin kalubalen da ke damun yankin mai arzikin man fetur.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Jimamin Hadarin Jirgin Ruwan Da Ya Janyo Asarar Rayukan Mutane Da Dama a Adamawa

Rahoto ya nuna cewa gangar man da Najeriya ke haƙowa a kowace rana ta faɗi ƙasa zuwa ganga 470,000 a watan Agusta, 2023, hakan na nufin kaso 23 cikin 100 ɓarayi ke sace wa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Muhimmin dalilin ziyarar da Ministan ya kai wa Jonathan

Ministan ya kai wa tsohon shugaban ƙasa Jonathan ziyara ta musamman domin neman shawarwarinsa kan yadda za a shawo kan baki ɗaya matsalolin da suka addabi yankin.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin ministan raya Neja Delta ta nuna cewa sun yi tattauna wa mai ma'ana da fahimta kan dabarun yaƙi da satar ɗanyen mai, gina ababen more rayuwa da samar da ayyuka ga matasa.

Wani ɓangaren sanawaran ya ce:

"A ranar Talata tsohon shugaban kasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya karbi bakuncin ministan a gidansa da ke birnin tarayya Abuja."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP Na Neman Dawowa Ɗanye, Tsagin Atiku Ya Maida Martani Mai Zafi Ga Wike

"Sun yi tattaunawa mai kima da fahimta, inda suka mai da hankali kan dabarun yaki da satar danyen mai, inganta ababen more rayuwa, da samar da ayyukan yi ga matasa a yankin Neja Delta."

Gwamna Sanwo-Olu Na Lagos Ya Rantsar da Kwamishinoni 37 da Hadimai

Rahoto ya nuna kwamishinoni 37 da masu bai wa gwamna shawara ta musamnan sun karbi rantsuwar kama aiki a jihar Legas.

An sha taƙaddama kan jerin sunayen kwamishinonin tsakanin gwamna Babajide Sanwo-Olu da majalisar dokokin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262