Kashim Shettima Ya Caccaki Masu Handame Kudaden Tallafin Mai, Ya Ce Su Na Kawo Cikas A Kasa

Kashim Shettima Ya Caccaki Masu Handame Kudaden Tallafin Mai, Ya Ce Su Na Kawo Cikas A Kasa

  • Kashim Shettima ya gargadi wadanda su ka handame kudaden tallafin mai a baya da cewa su na kawo cikas a tsare-tsaren gwamnati
  • Kashim ya bayyana haka ne yayin babban taron ci gaban tattalin arzikin kasar a birnin Tarayya, Abuja
  • Ya ce ba za su dawo baya ba kan cire tallafin mai saboda masu handame kudaden na yi wa gwamnati zagon kasa

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana yadda wasu ke neman tarwatsa tsare-tsaren gwamnatin Shugaba Tinubu.

Shettima ya ce wadanda ke handame kudin tallafi su na neman hanyar durkusar da gwamnati saboda bukatar kansu.

Kashim Shettima ya ce ba za a dawo da tallafin mai ba
Kashim Shettima Ya Caccaki Masu Handame Kudaden Tallafin Mai A Baya. Hoto: Sanata Kashim Shettima.
Asali: Facebook

Meye Kashim ya ce kan tallafin mai?

Kashim ya bayyana haka ne yayin babban taron bunkasa tattalin arziki karo na 16 a ranar Talata 5 ga watan Satumba a Abuja, PM News ta tattaro.

Kara karanta wannan

"Ba Mu Ba Ne": Manoma Sun Yi Martani Bayan Tinubu Ya Umarci Bankin CBN Ya Kwato Tiriliyan 1 Na Lamuni, Bayanai Sun Fito

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mataimakin shugaban kasar ya tura sako ga wadannan mutane inda ya ce babu ranar dawo da tallafin mai.

Ya ce:

"Mun san irin wannan matsaloli na iya faruwa, mun san yadda mutanen su ka ginu kan kudaden tallafi da ake samarwa.
"Za su yi duk abinda za su yi don kawo cikas, amma kamar yadda na fada ba za a dawo da tallafin mai ba."

Ya ce tsare-tsaren da Shugaba Tinubu ya kawo tuni su ka fara kawo sauyi a kasar da kuma ci gaba.

Ya kara da cewa a yanzu Gwamnatin Tarayya har ma da na jihohi sun fi samun kaso mai tsoka na kudade, cewar TheCable.

Meye Kashim ya ce kan amfanin kudaden tallafi?

Ya kara da cewa:

"Wadannan kudaden tallafi su na kawo sauyi a rayuwar 'yan Najeriya, a yanzu samun kudaden ya sa muna amfani da su yadda ya dace."

Kara karanta wannan

Kwanaki 100 Kan Mulki: Tarun Matsaloli 3 Da Ke Hana Shugaba Tinubu Sakewa Tun Bayan Hawanshi Mulki

Daga cikin jiga-jigan da su ka halarci taron akwai ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu da shugaban kwamitin kasuwanci, Sanata Osita Izunaso.

Sauran sun hada da mukaddashin gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Folashodun Shonubi da wakilin Bankin Duniya, Shubam Chaudhuri.

Kashim Ya Fadi Gaskiyar Zancen Abin da Zai Faru a Mulkinsu

A wani labarin, a yunkurin ragewa mutanen kasar nan dogon buri, an ji Kashim Shettima ya na cewa gwamnatin mai gidansa za ta fara mulki ne a kan gargada.

Da yake jawabi a laccar da aka shirya domin rantsar da sabon shugaban kasa, Kashim Shettima ya na fadan abin da ya kira gaskiyar zance.

Asali: Legit.ng

Online view pixel