Yayin Da Tinubu Ya Umarci Kwato Kudaden Noma A Wurin Jama’a, Kungiyar Manoma Ta Yi Martani

Yayin Da Tinubu Ya Umarci Kwato Kudaden Noma A Wurin Jama’a, Kungiyar Manoma Ta Yi Martani

  • Kungiyar Manoma a Najeriya (AFAN) ta yabawa shugaban kasa, Bola Tinubu kan matakin kwato kudaden noma
  • Sai dai kungiyar ta ce an tafka kuskure don ba manoma ba ne su ka ci wadannan kudade don ba a bi tsari ba wurin rabon kudaden
  • Arc Ibrahim Kabir, shugaban kungiyar shi ya bayyana haka inda ya shawarci Tinubu yadda za a bi nan gaba don inganta noma

FCT, Abuja – Kungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN) ta goyi bayan matakin Shugaba Tinubu na kwato basukan manoma na CBN.

Legit.ng ta tattaro cewa Tinubu ya umarci bankin CBN da hadin gwiwar jami’an tsaro don kwato kudaden kafin 18 ga watan Satumba.

Tinubu ya umarci kwato basukan noma a Najeriya
Tinubu Ya Umarci Kwato Kudaden Noma a Wurin Jama’a. Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Luis Tato.
Asali: Getty Images

Meye manoman ke cewa kan bashin Tinubu?

Shugaban kungiyar AFAN, Arc Ibrahim Kabir ya ce wadanda ba manoma ba ne su ka ci kudaden da ya kai Naira biliyan 2.6.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Sako Dakataccen Karamar Hukumar Jihar APC da Ta Tsare, Bayanai Sun Fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce tabbas dawo da kudaden zai ba da wahala ganin wadanda su ka lankwame kudaden ba manoma ba ne.

Ya bayyana cewa a lokacin raba kudaden ba a tuntubi kungiyar ba shi yasa aka samu matsala, cewar Vanguard.

Ya ce:

“Da farko an dauko abin gwanin sha’awa amma daga baya aka samu matsala saboda rashin tsari.
“Tun farko ya kamata ma’aikatar noma ta dauki abin sannan ta hada akai da kungiyar AFAN don binciko manoma na hakika don amfanar mutane.”

Wane shawara manoman su ka bai wa Tinubu?

Ya kara da cewa:

“Yawan kudaden da aka ware ya fi karfin harkar noma, madadin kawo sauki a samar da abinci sai hakan ya kara tashin farashin kayayyaki.”

Kabir ya yabi Tinubu kan wannan shiri na shi inda ya ce sai dai kwato kudaden tabbas zai ba da wahala matuka.

Kara karanta wannan

Karauniya Yayin Da Aka Sanar Da Sabon Farashin Gas Sabanin Yadda Tinubu Ya Yi Alkawari A Baya, Bayanai Sun Fito

Ya shawarci gwamnati ta yi amfani da bankin noma na BOA don binciko asalin manoma tare da ba su bashin kudaden don ganin an samu abin da ya dace.

Kabir ya yi alkawarin cewa kungiyarsu za ta samar da bayanai na manoma da kuma inda gonakinsu su ke yayin ba da tallafin don inganta harkar noma.

CBN Zai Damke Wadanda Su Ka Ki Biyan Bashin Noma

A wani labarin, Babban bankin Najeriya CBN ya ce zai fara kamen manoman da su ka karbi bashin gwamnati da ba su biya ba don taimakawa wasu a gaba..

Gwamnatin Tarayya ta bai wa manoma lamunin irin shinkafa da tsirrai da kuma kudade don inganta harkokin noma a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel