Yan Sanda Sun Kama Mutum Daya Da Ake Zargi Da Hannu a Kisan Babbar Alkali a Benue

Yan Sanda Sun Kama Mutum Daya Da Ake Zargi Da Hannu a Kisan Babbar Alkali a Benue

  • Hukumar 'yan sanda ta yi nasarar kama mutum ɗaya da ake zargi da hannu a kisan wata babbar Alkali mai ritaya a jihar Benuwe
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Catherine Anene, ta bayyana cewa an kama wanda ake zargin da wasu abubuwa
  • Kwamishinan 'yan sanda ya aike da saƙon ta'aziyya ga baki ɗaya iyalan mamaciyar tare da alƙawarin kamo duk mai hannu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Benue state - Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Benuwe ta cafke mutum guda da take zargin yana da hannu a laifin kashe wata alkali mai ritaya, mai shari’a Margaret Igbetar.

Jaridar Punch ta ruwaito yadda aka tsinci gawar shugabar kotun daukaka kara ta Kostumare a jihar Benuwe mai ritaya a ranar Alhamis a gidanta da ke birnin Makurɗi.

Kwamishinan yan sandan jihar Benuwai, Bartholomew Onyeka.
Yan Sanda Sun Kama Mutum Daya Da Ake Zargi Da Hannu a Kisan Babbar Alkali a Benue Hoto: punchng
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa an tsinci gawar shugabar Kotun a cikin jini, kuma yanayin gawar ya nuna ba a ranar aka kashe ta ba.

Kara karanta wannan

Gunin Sha'awa: 'Yar Sanda Mace Ta Samu Kyauta Mai Tsoka Kan Ƙin Karɓan Maƙudan Kuɗin Cin Hanci

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Catherine Anene ta fitar ranar Asabar, hukumar ‘yan sandan ta bayyana cewa an kama wani mai suna, Aondohemba Joseph.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A rahoton Daily Trust, wani sashin sanarwan ya ce:

"A ranar 24 ga watan Agusta, 2023, jami'an 'yan sanda na caji ofis din 'E' da ke Makurɗi, suka samu labarin cewa Mai shari'a Margaret Mary Igbetar (mai ritaya) ta ɓata kuma bata amsa kiran waya."
"Nan take aka tura jami'ai su gudanar da bincike, suna tsaka da bincike a gidanta da ke layin Wantor Kwange kusa da titin Gboko a Makurɗi suka tsinci gawarta cikin jini a ɗakin girki."
"Binciken da aka yi ya kai ga kama wani Aondohemba Joseph tare kwato wasu abubuwa daga hannunsa domin ƙara zurfafa bincike."

Kara karanta wannan

Shugaban 'Yan Bindiga Ya Ayyana Kansa a Matsayin Gwamnan Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

Hukumar yan sanda ta yi wa iyalai ta'aziyya

PPRO ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Benuwai, CP Bartholomew Onyeka, ya aika sakon ta’aziyya ga dangi, kana ya yi Allah wadai da wannan ɗanyen aikin.

CP ya tabbatar wa Iyalin mamaciyar cewa zai yi duk mai yiwuwa don tona asirin duk wanda ke bayan kisan tare da gurfanar da su a gaban ƙuliya, Tribune ta tattaro.

Kwamishinan Anambra Ya Bai Wa Yar Sanda Kyautar N250,000

A wani rahoton na daban Kwamishinan 'yan sanda ya bai wa jami'ar 'yan sanda mace kyautar N250,000 bisa nuna gaskiya da rikon amana a bakin aiki.

Insufekta Charity Oyor ta samu wannan kyauta sakamakon ƙin karban cin hanci daga wanda ake zargi a jihar Anambra.

Asali: Legit.ng

Online view pixel