Masu Shirin ‘Mata A Yau’ Sun Ziyarci Malam Daurawa Domin Bayar Da Hakuri Ga Al'umma

Masu Shirin ‘Mata A Yau’ Sun Ziyarci Malam Daurawa Domin Bayar Da Hakuri Ga Al'umma

  • Matan da ke gabatar da shirin 'Mata A Yau' a gidan talabijin na Arewa24 sun ziyarci Sheikh Daurawa Kano
  • Ziyarar ta su na zuwa ne a daidai lokacin da ake tafka muhawara kan kalaman da suka yi a cikin shirin
  • Sun bai wa al'ummar da maganganun na su suka ɓatawa rai haƙuri, tare da bayyana cewa ba abinda suke nufi ba kenan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - A makon da ya gabata ne dai kafafen sada zumunta a Arewacin Najeriya suka cika da zazzafar muhawara kan wani shiri mai take 'Mata A Yau' da ake gabatarwa a gidan talabijin na Arewa24.

Hakan ya samo asali ne daga bayanin da ɗaya daga cikin masu gabatar da shirin, Aisha Umar Jajere ta yi dangane da batun gaisuwa tsakanin mata da miji.

Kara karanta wannan

Albashi Da Allawus Din Ministocin Tinubu Ya Bayyana, Za Su Lakume Biliyan 8.6

Masu gabatar da shirin Mata A Yau sun ziyarci Daurawa
Masu gabatar da shirin 'Mata A Yau' sun ziyarci Daurawa, sun bai wa al'umma haƙuri. Hoto: Naxeer Kaoje
Asali: Facebook

Abinda aka fadi a shirin Mata A Yau

A cikin wani ɗan gajeren bidiyo da aka wallafa a shafin 'Mata A Yau' na Facebook, an ga ɗaya daga cikin matan na cewa, idan mata ba ta gaishe da mijinta ba shi sai ya gaisheta, wanda hakan ne ya janyo zazzafar muhawara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Malamai da dama a ciki da wajen birnin Kano, sun yi martani mai zafi dangane da wannan kalami da ma sauran abubuwan da aka gabatar a shirin.

Haka nan ma ma su amfani da kafafen sada zumunta musamman ma Facebook a Arewacin Najeriya, sun caccaki masu gabatar da shirin inda mafi yawa ke ganin hakan na iya janyo rigingimu a tsakanin ma'aurata.

Masu shirin Mata A Yau sun ziyarci Daurawa, sun nemi Hisbah ta sa baki

Kara karanta wannan

“Ina Dalili”: Suka, Martani Kan Nadin Hadimai Mata 131 Da Gwamnan Arewa Ya Yi

Biyo bayan suka da masu gabatar da shirin suka sha daga ɓangarori daban-daban, sun kai ziyara wajen kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.

Sun bayyana cewa kuskure aka samu, amma ba abinda suke son isarwa ba kenan, inda suka bayyana cewa hankalinsu ya tashi sosai kan yadda jama'a suka taso mu su.

Fitaccen malamin nan na addinin Musulunci, Sheikh Adam Abdallah Adam ne ya bayyana hakan a cikin wani ɗan gajeren bidiyo da wani mai amfani da kafar X, @A_Y_Rafindadi ya wallafa.

Ya ce sun nemi al'ummar Musulmin da kalaman da suka yi a cikin shirin suka ɓatawa rai da su yi haƙuri.

Budurwa ta maka saurayi gaban kotu bisa zargin yaudara a Kano

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wata budurwa da ta maka saurayinta a gaban wata kotun majistare da ke zamanta a garin Kano ta Dabo.

Kara karanta wannan

Wike Ya Jero Mutanen Da Zai Cusa Kafar Wando Daya Da Su Bayan Zama Minista

Budurwar ta yi zargin cewa saurayin na ta ya yaudareta bayan gama kashe ma sa maƙudan kuɗaɗe da ta yi a baya, inda ta nemi a bi ma ta haƙƙinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel