An Caccaki Gwamna Bago Na Neja Saboda Nada Sabbin Hadimai Mata 131 Da Ya Yi

An Caccaki Gwamna Bago Na Neja Saboda Nada Sabbin Hadimai Mata 131 Da Ya Yi

  • 'Yan Najeriya sun tattake wuri kan nadin hadimai 131 da gwamnan Neja Umar Bago ya yi
  • Wasu sun caccaki gwamnan kan rashin la'akari da halin matsin da ake ciki kafin ba da muƙaman
  • An bayyana cewa 90 daga cikinsu masu ba da shawara na musamman ne, yayin da 41 kuma kodinetoci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Minna, jihar Neja - Gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, ya naɗa mata 131 a matsayin masu ba shi shawara na musamman.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnan ya fitar ranar Asabar, 19 ga watan Agusta a gidan gwamnatin jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Umaru Bago ya naɗa mata 131 muƙaman gwamnati
Gwamna Umaru Bago ya sha suka kan naɗin mata 131 da ya yi. Hoto: Umaru Mohammed Bago
Asali: Facebook

Aikin da mata 131 da gwamna Bago ya naɗa za su yi

A cikin jawabin an bayyana cewa 90 daga cikin matan da aka naɗa za su yi aiki ne a matsayin masu ba gwamnan shawara na musamman, yayin da ragowar 41 za su yi aiki a matsayin kodinetoci.

Kara karanta wannan

Wike Ya Jero Mutanen Da Zai Cusa Kafar Wando Daya Da Su Bayan Zama Minista

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakataren gwamnatin jihar, Abubakar Usman, ya bayyana cewa an yi duka naɗe-naɗen da aka yi ne bisa cancanta da gogewa.

Usman ya ƙara da cewa akwai tsare-tsare na mata da gwamnatin jihar ta zo da su, wanda a dalilin hakan ne aka bai wa mata muƙaman domin a samu abinda ake so.

Ya yi kira ga matan da aka naɗa da su yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen ganin sun kawowa jihar Neja ci gaba kamar yadda TheCable ta wallafa.

Martanin 'yan Najeriya kan naɗin mata 131 da gwamnan Neja ya yi

Masu amfani da kafar sada zumunta ta X da dama sun tofa albarkacin bakunansu dangane da wannan naɗi da Gwamna Umaru Bago ya yi.

A yayin da wasu suka yaba ma sa kan sanya mata da dama cikin gwamnatinsa da ya yi, wasu na ganin cewa hakan bai kamata ba duba da halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

"Ba Zan Yi Karya Domin Kare Gwamnatin Tinubu Ba" Sabon Minista Ya Yi Magana Mai Jan Hankali

@oshkunlery ya ce:

“Za a iya kawar da kai a kan kodinetoci 41, amma SSA 90 akan wane dalili? Barnatar da kuɗaɗen tallafin da Gwamnatin Tarayya ta bayar.”

@bra_zac ya ce:

“Duk abinda zai yi a kan mata a banza, muddun zai riƙa tausayawa 'yan ta'adda. 'Yan ta'addan da suka kashe mutane da dama ciki har da sojoji 31 na kwanan nan, wanda hakan ya mayar da mata da yara zawarawa da marayu.”

Gwamnan Neja na duba yiwuwar zama da 'yan bindiga

A rahoton da Legit.ng ta kawo a baya, gwamnan jihar Neja Mohammed Umaru Bago, yana duba yiwuwar zama domin tattaunawa da 'yan bindigar da suka addabi jihar.

Hakan ya biyo bayan hare-hare ba ƙaƙƙautawa da 'yan bindigan ke kai wa a sassa daban-daban na jihar a cikin 'yan kwanakin nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel