“A Raba Aurenmu Dukana Take Yi”: Magidanci Ya Maka Matarsa a Kotu

“A Raba Aurenmu Dukana Take Yi”: Magidanci Ya Maka Matarsa a Kotu

  • Wani magidanci ya maka matarsa a gaban kotu bisa zarginta da yake da cin mutuncinsa
  • Raphael Chima ya bayyanawa kotu cewar matarsa Joy na yawan marinsa sannan ta jibge shi a duk lokacin da ta samu damar yin hakan
  • Ya roki alkalin kotun da ke babban birnin tarayya da ya taimaka ya raba auren nasu sannan ya mika masa ragamar kula da 'da daya tilo da suka haifa tare

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Wani dan kasuwa mai suna Raphael Chima, ya maka matarsa, Joy, a gaban kotun gargajiya da ke Jikwoyi, babban birnin tarayya Abuja saboda tana yawan jibgarsa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa Raphael ya yi zargin ne a cikin wata kara na neman a raba aurensu da Joy wanda ya shigar a gaban kotun.

Kara karanta wannan

Mace ta yi Karar Saurayi a Kotu, Ya Yaudare ta Bayan ta Kashe Masa N0.9m a Kano

Sandar kotu
“A Raba Aurenmu Dukana Take Yi”: Magidanci Ya Maka Matarsa a Kotu Hoto: Thisday
Asali: UGC

Ya ce:

"Matata na buguna da cin zarafina, tana marina da zaran ta samu dama. Tana rikirkita tunanina."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma sanar da kotun cewa matar tasa bata ganin mutuncin iyayensa da suka haife shi, rahoton Nigerian Tribune.

Har ila yau, wanda yake karan ya sanar da kotun cewa matar ta dade da yin watsi da 'da daya da suka haifa kuma cewa shine yake kula da shi.

Ya roki kotun da ta raba auren nasu sannan ta daura masa alhakin kula da dan nasu.

Sai dai kuma wacce ake karar, Joy, ta musanta dukkanin zarge-zargen da mijinta ke yi a kanta.

Ku je ku sasanta kanku, Alkali ga ma'auratan

Mai shari'a Dada Oluwaseyi ya shawarci ma'auratan da su rungumi sulhu a tsakaninsu.

Oluwaseyi ya dage ci gaba da sauraron karar domin samun rahoton sasantawa ko kuma sauraron karar.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Asari Dokubo Ya Sha Alwashin Yin Kasa-Kasa Da Gwamnatin Sojan Nijar

Dan jihar Adamawa Musulmi ya angwance da tsaleliyar baturiya kirista

A wani labari na daban, mun ji cewa Isa Hammanjoda, dan shekaru 39 daga jihar Adamawa da ke Najeriya bai taba tunanin soyayya da wata mace daga kasar waje ba.

Ya hadu da Diana Maria Lugunborg, mai shekaru 43 kuma malamar makarantar Firamare ta hannun wata aminiyarta, Ramata Ahmadou, wacce ta auri abokinsa, Mohammed Umar, bayan sun hadu a soshiyal midiya.

Ramata, wacce ita ma take aikin koyarwa a Norway, ta nunawa kawayenta hotunan aurenta a Najeriya sannan Diana ta ci karo da fuskar Isa a wani hoto da suka yi cikin jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel