Kwamacala: Matar aure ta gaji da zama da mijinta ta fita taje tana soyayya da mata da miji a lokaci guda

Kwamacala: Matar aure ta gaji da zama da mijinta ta fita taje tana soyayya da mata da miji a lokaci guda

- Wata mata mai 'ya'ya hudu ta bar gidan mijinta ta fita tana soyayya da wani mutumi da matarshi a lokaci guda

- Sakamakon wannan lamari yanzu yaran nata guda hudu suna kiran sabon saurayintan da wani irin suna daban

- Duk da dai cewa matar da sabon saurayintan basu bayyana ko zasu haihu tare ba, amma hakan bai hana su kusantar juna ba

Wata mata mai 'ya'ya hudu mai suna Emma Fedigan, ta gaji da zaman gidan mijinta, inda ta fita ta fara soyayya da wani mutumi da matarshi a lokaci daya. Hakan ya sanya 'ya'yan suka fara kiran saurayintan da wani suna daban.

Jaridar The Sun UK ta ruwaito cewa Emma da tsohon mijinta Robert sun fara soyayya tun suna 'yan shekara 20, kuma ta sanar dashi yadda take son namiji ya dinga kwanciya da ita tun kafin suyi aure.

Kwamacala: Matar aure ta gaji da zama da mijinta ta fita taje tana soyayya da mata da miji a lokaci guda
Kwamacala: Matar aure ta gaji da zama da mijinta ta fita taje tana soyayya da mata da miji a lokaci guda
Asali: Facebook

Sai dai Emma ta ce bata samu abinda take so ba a rayuwa sakamakon yaran da suka haifa tana bata lokaci wajen lura da su.

A lokacin da ma'auratan suka yanke shawarar fita neman masoya, sun hadu da wasu ma'auratan Simon Berry da matar shi Kelly.

KU KARANTA: Yadda na zama direban jirgin sama daga aikin tura baro - Dan Najeriya ya bada labari mai ban sha'awa

A shekarar 2019, soyayyar dake tsakanin Emma da Kelly ta kare hakan ya sanya dole ta koma ga tsohon mijinta.

"Ina matukar jin dadin soyayyar da nake yi da Simon, munyi aure da Robert tun a shekarar 2006. Rob shine rabin rayuwata ba zan iya rayuwa babu shi ba, amma babu adalci ace koda yaushe daya ne a cikin mu zai nemi ya biya bukatar daya. Soyayya nada fadi ba zai yiwu ka so mutum daya ba kawai," ta ce.

Sai dai kuma bayan tattaunawa mai tsawo, Emma ta samu sun sake daidaitawa da Simon, kamar yadda mutumin ya ce: "Bani da niyyar bari dangantakar dake tsakanina da Emma ta tafi ba tare dana yi wani abu a kai ba, saboda na san cewa magana nada matukar muhimmanci, bayan mako daya nace mata ina so mu hadu."

Duk da dai wasu daga cikin abokanan Emma suna goyon bayan dangantakar dake tsakaninsu, da yawa daga cikin 'yan uwanta sun nuna rashin amincewarsu, inda ita kuma ta ja baya da su.

Duk da dai masoyan basu da niyyar haihuwa a yanzu, amma Emma ta ce akwai yiwuwar za su haihu nan gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel