Sarkin Zazzau Ya Maye Gurbin Munir Jafaru da Madaki Ya Ajiye Mukaminsa

Sarkin Zazzau Ya Maye Gurbin Munir Jafaru da Madaki Ya Ajiye Mukaminsa

  • Alhaji Muhammadu Munnir Ja’afaru ya bar hakimcin kasar Basawa tun a karshen watan Yulin 2023
  • Madakin Zazzau ya aika takardar murabus zuwa ga Mai martaba Sarki Malam Ahmed Nuhu Bamalli
  • Sarki ya nada Barde Kerrariyyan Zazzau ya zama sabon Hakimi wanda kafin yanzu yake Zangon Aya

Kaduna - Muhammad Munir Ja’afaru ya sauka daga kujerar da yake kai ta Hakimin Basawa a kasar Zazzau.

Bayanai sun kara fitowa fili cewa Muhammad Munir Jafaru wanda shi ne Madakin Zazzau ya yi murabus ne saboda sabani da aka samu.

Daily Nigerian ta ce tsohon Hakimin ya na zargin an shiga huruminsa a kan abin da ya shafi nadin Mai gari, saboda haka ya bar matsayinsa.

Sarkin Zazzau
Madakin Zazzau, Maniru Jafaru Hoto:Bashir Umar Fagachi
Asali: Facebook

Nadin Dagaci a Zazzau

Munir Ja’afaru wanda ya rike Yariman Zazzau na tsawon shekaru, ya na cikin wadanda su ka nemi sarauta bayan rasuwar Shehu Idris.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: "Yan Ta'adda Sun Tsorata Tun Bayan Nadin Matawalle Karamin Ministan Tsaro", Kaura Ya Yi Bayani

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mahaifinsa watau Jafaru Dan Isiyaku wanda ya fito daga gidan bare-bari ya yi shekaru fiye da 20 a sarautar Zazzau kafin rasuwarsa a 1959.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa Hakimin ya hakura da kujerarsa ne bayan Mai martaba Ahmed Bamalli ya ki amincewa da nadin da ya yi.

Bisa al’ada, Hakimi yake da ikon zaben dagaci a garuruwansa, daga nan kuma sai Sarkin ya nadawa wanda aka zaba rawani a cikin fadarsa.

Za ayi nadin sarauta babu Munir Jafaru

A wannan karo da aka gabatar da wanda zai rike sarautar Unguwar Gwaiba a gaban Sarki Zazzau domin ya amince da shi, sai aka samu matsala.

Mai martaba Ahmed Bamalli ya yi korafin rashin ganin Hakimin Basawa a zauren, sai ya bukaci a cire rawanin Mai unguwar, ba a iya nada shi ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Dauko Matasa ‘Yan Shekara 26 da 32, Ya Damka Masu Mukamai a Katsina

A wani rahoto da aka samu a Daily Trust, kakakin masarautar Zazzau, Abdullahi Aliyu Kwarabi ya tabbatar da canjin da aka samu a gundumar.

Ba tare da ya fadi dalili ba, Kwarbai ya shaida cewa Sarki ya amince da murabus din Madaki kuma ya nada wanda zai zama sabon hakimi a Basawa.

Da karbar wasikar Muhammadu Munnir Jafaru sai Sarki ya amince da Hakimin Zangon Aya, Haruna Abubakar Bamalli, ya maye gurbin shi.

Taron dangin siyasa

A fagen siyasa kasa, an samu rahoto ‘Yan takaran Shugaban kasa a zaben 2023 su na so su yi wa jam’iyyar APC taron dangi domin su karbe mulki.

Babu tabbacin hadin-kan zai yiwu domin tattaunawar NNPP-LP ba ta je ko ina ba tsakanin bangaren Rabiu Musa Kwankwaso da kuma Peter Obi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel