Sarautar Zazzau: Tsaro ya tsananta a gidan Yariman Zazzau, Mannir Jaafaru

Sarautar Zazzau: Tsaro ya tsananta a gidan Yariman Zazzau, Mannir Jaafaru

- Sakamakon rashin sarkin Zazzau da aka yi a ranar 20 ga watan Satumba, karagar mulkin kasar Zazzau ta zama abun nema

- An gano cewa, tsaro ya matukar tsananta a gidan Yariman Zazzau, Alhaji Munir Jaafaru, da ke GRA Zaria

- An gano cewa, gwamnan Kaduna ya karba fasfoti, takardun haraji da sauran takardu masu muhimmanci daga Yariman Zazzau

Akwai rade-radin da ke yawo a kasar Zazzau cewa gwamnatin jihar tana hararo nada Yariman Zazzau, Munir Jafaru a matsayin sabon sarkin Zazzau, lamarin da yasa aka tsananta tsaro a gidansa da ke Zaria.

Karagar mulkin Zazzau ta zama abun nema tun bayan rasuwar sarkin Zazzau na 18, Alhaji Shehu Idris a ranar 20 ga watan Satumban 2020.

Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa gwamnatin jihar Kaduna ta karba fasfoti, takardun haraji da sauran wasu takardu masu amfani daga hannun Jaafaru.

Majiyoyi sun tabatar da cewa, jama'a suna ta tururuwar zuwa gidan Jaafaru domin mika sakon taya murnarsu garesa.

Duk da gwamnatin jihar Kaduna bata sanar ba, majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa, wasu jiga-jigai a kasar nan suna kira ga gwamnan da ya nada Jaafaru.

"Yarima shine dan takara da jama'a suka fi so. Ko da kuwa za a bi jama'a a ce su zaba mutum daya a cikin 'yan takarar, Munir za su zaba," wata majiya daga fada ta sanar.

KU KARANTA: Hotunan sojoji, 'yan sanda da jami'an CTJF da 'yan Boko Haram suka ragargaza a tawagar Zulum

Sarautar Zazzau: Tsaro ya tsananta a gidan Yariman Zazzau, Munir Jafaru
Sarautar Zazzau: Tsaro ya tsananta a gidan Yariman Zazzau, Munir Jafaru. Hoto daga @Dailynigerian
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram tare da iyalansu sun mika wuya ga dakarun soji a Banki (Hotuna)

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna ba za ta yi amfani da rahoton da majalisar nadin sarki na masarautar Zazzau ta kai mata ba domin cike gurbin sarkin Zazzau, wata majiya da ta san kan lamarin ta tabbatar wa da Premium Times.

Wannan hukuncin ya dawo da Ahmed Bamalli, wanda aka tabbatar da cewa Gwamna Nasir El-Rufai ke so a cikin masu zawarcin karagar mulkin.

Premium Times ta gano cewa, gwamnan ya yanke wannan hukuncin bayan zargin da yayi an bai wa wasu daga cikin 'yan majalisar cin hanci.

A farkon makon nan ne aka gano cewa, 'yan gidajen sarautu hudu ne daga gidaje uku na sarautar Zazzau suka fito neman kujerar.

Sun hada da Iyan Zazzau, Bashir Aminu; Magajin Garin Zazzau, Ahmed Bamalli; Yeriman Zazzau, Munir Ja’afaru da Turakin Zazzau, Aminu Idris. Daga cikin mutum hudun, 'yan majalisar sun mika sunayen mutane uku inda Ahmed Bamalli bai samu shiga ba.

Wata majiya daga fadar ta tabbatar da cewa, sunan Ahmed Bamalli bai shiga jerin bane saboda hatta kakansa bai yi sarautar Zazzau ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel