Da duminsa: Allah ya yi wa Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, rasuwa

Da duminsa: Allah ya yi wa Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, rasuwa

- Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, Allah ya yi wa Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris rasuwa

- Sarkin Zazzau Shehu Idris ya rasu yana da shekaru 84 a duniya bayan gajeriyar rashin lafiya

- Mai martaba marigayin Sarkin, shine sarki na 18 na Fulani a masarautar Zazzau

Labari da duminsa da ke zuwa wa Legit.ng a yanzu shine rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.

Majiyoyi da dama da suke da kusanci da fadar sarkin sun tabbatar da rasuwarsa a yau Lahadi.

Marigayi Sarkin Zazzau shine Sarki na 18 na Fulani a masarautar Zazzau. Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.

Majiyoyi da dama sun tabbatar wa Legit.ng cewa, basaraken ya rasu a asibitin 44 da ke Kaduna wurin karfe 11 na safiyar Lahadi.

"Tabbas Allah ya yi wa Sarki rasuwa. Ya kwanta rashin lafiya tun a ranar Juma'a kuma an kai shi asibiti inda ya rasu.

"Nan babu dadewa za a dawo da gawarsa Zaria domin fara shirin jana'izarsa," wata majiya mai kusanci da Iyan Zazzau ta tabbatar.

Da duminsa: Allah ya yi wa Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, rasuwa
Da duminsa: Allah ya yi wa Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, rasuwa. Hoto daga Abdul'aziz Umar
Source: Facebook

Karin bayani na nan tafe...

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel