Jerin abubuwan da Sarki Ahmad Bamalli ya yi tun da ya hau kan karagar mulki

Jerin abubuwan da Sarki Ahmad Bamalli ya yi tun da ya hau kan karagar mulki

- A watan Oktoban 2020 ne Ahmed Nuhu Bamalli ya zama Sarkin Zazzau

- Ahmed Bamalli ya zama Sarkin farko daga Mallawa cikin shekara 100

- Kwanan nan sabon Sarki ya fitar da jerin nadin sarautar farko da ya yi

A makon da ya wuce aka cika kwanaki 100 da Mai martaba Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya zama Sarkin Zazzau.

A ranar Laraba, 7 ga watan Oktoba, 2020, Ahmed Nuhu Bamalli ya gaji Alhaji Shehu Idris a kan karagar Sarkin Zazzau.

Mun tattaro wasu daga cikin sauye-sauyen da aka samu a wannan masarauta bayan lokacin da Ahmed Bamalli ya zama Sarki.

1. Yi wa gidan Bare-bari babban nadi

A watan nan ne Mai martaba Sarki ya amince da nadin Yariman Zazzau, Mannir Jafaru, a matsayin Madakin Zazzau. Wannan babbar sarauta ce wanda ta saba fitowa cikin ‘ya ‘yan Sarki.

KU KARANTA: Sarkin Zazzau ya yi sababbin nade-naden farko a gadon mulki

2. Karbe sarautar Iyan Zazzau

Mai martaba Ahmed Bamalli ya karbe sarautar Iya daga gidan Katsinawa jim kadan bayan rasuwar Alhaji Bashir Aminu. Wannan sarauta ta koma gidan Abbas Tajuddeen na Mallawa.

3. Magajin Garin Zazzau

Sabon sarki ya bada sarautarsa ta Magajin Gari ga ‘danuwansa, Mansur Nuhu Bamalli. Mai martaba ya tsallake mai bi masa a gidan Nuhu Bamalli, ya dauko Barde Kerarriya.

4. Maye gurbin wadanda suka rasu

Bayan Iyan Zazzau, Ahmed Bamalli ya nada sababbin Sa’i da Talban Zazzau bayan rasuwar wadanda su ke rike da wannan mukamai. Talba ya koma gidan Iya Bashar Aminu.

Jerin abubuwan da Sarki Ahmad Bamalli ya yi tun da ya hau kan karagar mulki
Sarkin Zazzau Ahmad Bamalli Hoto: Facebook Daga: PrinceofZazzau
Asali: Facebook

KU KARANTA: Takaitaccen tarihin Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli

5. Sauran nade-nade

Ragowar wanda Mai martaba ya ba sarauta sun hada da Idris Ibrahim Idris, Shehu Tijjani, Abdulkarim Bashir Aminu, Bashir Abubakar, Buhari Ciroma da Aminu Iya Sa’idu.

Za su rike sarautan Sa’i, Barde, Barden Kudu, Barde Kerarriya da kuma Kogunan Zazzau.

Idan za ku tuna Allah ya yi wa Alhaji Bashir Aminu, Iyan Zazzau rasuwa a farkon shekarar nan.

Alhaji Bashir Aminu ya rasu ne a sakamakon gajerar rashin lafiya da yayi. Wata majiyar ta kuma bayyana mana cewa Sarakin bai yi fama da wata jinya kafin ya cika a Legas ba.

Marigayi Iya ya na cikin wadanda suka nemi saurautar Zazzau, kuma a karshe Aminu Bashir ya yi karar gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a kotu a kan nadin da ya yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng