Gwamnan Katsina Ya Dauko Matasa ‘Yan Shekara 20 da 30, Ya Damka Masu Mukamai

Gwamnan Katsina Ya Dauko Matasa ‘Yan Shekara 20 da 30, Ya Damka Masu Mukamai

  • Dikko Umaru Radda ya na cigaba da rabon mukamai, matasa su na samu kujera a gwamnatinsa
  • Gwamnan jihar Katsina ya nada Naufal Ahmed ya jagoranci sashen kimiyya da fasaha da aka kafa
  • Wani matashi da aka ba kujerar mai ba Gwamnan Katsina shawara shi ne Muhammad Nagaske

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Katsina - A karshen makon jiya ne aka ji Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda ya ba Naufal Ahmed mai shekara 32 mukami a gwamnati.

Wata sanarwa da aka samu daga ofishin babban Mai taimakawa gwamnan a kan kafofin sadarwa na zamani ta tabbatar da haka a shafin X.

Hadimin gwamna Dikko Umaru Radda, Malam Isah Miqdad ya ce Naufal Ahmed ya zama Darekta Janar na sashen fasahar zamani da aka kafa.

Gwamnan Katsina
Naufal, Gwamna Dikko Umaru Radda, Ph.D., Nagaske Hoto: @dikko_radda, @Miqdad_Jnr
Asali: Twitter

Gwamna ya yarda da Naufal Ahmed

Mai girma gwamnan ya sa hannu a takardar nadin mukamin tun ranar 14 ga Agustan 2023.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Gwangwaje Sojojin Da Suka Ji Rauni Da Kyautar Kudi Masu Yawan Gaske

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta ce Malam Dikko Umaru Radda, PhD ya gamsu Naufal mai shekara 32 a duniya zai yi aiki da kyau tare da nuna kishin jihar Katsina.

Kafin ba shi wannan mukami, Naufal ya samar da cibiyar fasaha ta farko a yankin mai suna Kirkira, kokarin da ya jawo masa yabo cikin matasa.

...da Amb. Muhammad Nuhu Nagaske

A baya Legit.ng Hausa ta nada labari gwamnan da ya hau mulki a Mayun bana ya zabi Muhammad Nuhu Nagaske ya zama Mai ba shi shawara.

Tun a karshen watan Yuli ake sa ran Muhammad Nagaske ya shiga ofis a matsayin wanda zai rika taimakawa gwamna a kan sha’anin dalibai.

Gwamnan Katsina ya tafi da mata

Kokarin gwamnan na ganin ya tafi da mata da matasa bai tsaya a nan, ya ba mata uku mukamai.

Kara karanta wannan

A'a ba laifinmu ba ne: Sanata Ya Fadi Wadanda Su Ka Hana El-Rufai Zama Minista

A wata sanarwa ta dabam, an ji Jari Bala Batsari, Hajia Jamila Tama da Hajia Mami Lawal sun shiga cikin masu taimakawa Dikko Umaru Radda.

Wadannan mata za su wakilci yankunansu wajen ba gwamnan Katsina shawara a kan harkokin siyasa bayan matan da su ka zama kwamishinoni.

Za a nada Dangiwa da Musawa Minista

Rahotanni sun tabbatar da tsohon sakataren gwamnatin Katsina Ahmed Dangiwa zai zama Ministan gidaje da raya birane a gwamnatin Bola Tinubu.

Tsohon mataimakin gwamnan Kano, Abdullahi T. Gwarzo zai zama mataimakinsa. Hannatu Musawa daga jihar Katsina ta na cikin jerin ministocin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel