Atiku, Kwankwaso da Obi Su Na Tattaunawa Domin Kafa Gagarumar Jam’iyyar Adawa

Atiku, Kwankwaso da Obi Su Na Tattaunawa Domin Kafa Gagarumar Jam’iyyar Adawa

  • Babu mamaki Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi su dunkule a rumfar siyasa guda
  • Ana jita-jita cewa mutanen ‘dan takarar PDP a zaben 2023 sun hadu da jagoran Kwankwasiyya
  • Idan an samu yadda ake so a kotu, magoya bayan PDP, LP da NNPP za su yi wa APC taron dangi

Abuja - Ganin yadda ake ciki a siyasar Najeriya, rahotanni sun fara nuna yiwuwar dunkulewar Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi.

Labari ya fito daga This Day cewa manyan ‘yan takaran jam’iyyun adawan da aka gwabza da su a zaben 2023 za su iya shigewa cikin rumfa guda.

Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi sun fara tattaunawa a game da yiwuwar su hada-kai da nufin kifar da gwamnatin APC a kasar.

Obi, Kwankwaso, Abubakar
Atiku, Kwankwaso da Obi za su yaki Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu ya koyawa 'Yan adawa hankali

Kara karanta wannan

Makiyinka Zai Iya Zama Masoyi: El-Rufai Ya Yi Shagube a Twitter Kafin Nadin Ministoci

Ganin yadda zaben shugaban kasa da aka yi a farko shekarar nan ya ladabtar da su, ‘yan takaran na PDP, LP da kuma NNPP sun fara neman mafita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce ba yanzu jagororin siyasar nan su ka fara wannan zama ba, burinsu shi ne a kawo karshen APC da ta ke rike da mulki tun Mayun 2015.

An yi zaman farko ne tsakanin Atiku Abubakar da Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya yi takara a NNPP, kuma ya zo na uku da rata mai yawa sosai.

...An shigo da Peter Obi

Bayan an ga alamun nasara daga nan ne sai aka zauna da jagoran tafiyar Obidient, Peter Obi. Tashar talabijin Arise ta fitar da wanann rahoto a yau.

Kusoshin jam’iyyar PDP da masu ruwa da tsaki a NNPP sun ga bukatar a tuntubi ‘dan takaran na LP wanda ya girgiza siyasar Najeriya a zaben bana.

Kara karanta wannan

Meye zai faru? Shugaban matasan PDP ya bayyana kwarin gwiwar tsige Tinubu a mulki

Shari'ar zaben Shugaban kasa na 2023

Matsayar da aka tsaida a zaman da aka yi shi ne a fara jiran hukuncin da kotun sauraron korafin zabe za ta tanke, daga nan a yanke mataki na gaba.

‘Yan adawan su na fatan alkalan kotun korafin zaben shugaban kasar za su rusa nasarar Bola Tinubu, sun kira hakan da shi ne adalci da gaskiya.

Muddin kotu ta tsaida cewa a shirya sabon zabe, sai tsohon mataimakin shugaban Najeriya da jagororin Kwankwasiyya da Obidient su hada-kansu.

Idan kuwa ba ayi nasara a kotu ba, sai a fara shirin kafa babbar jam’iyyar adawa domin zaben 2027, inda PDP, LP da NNPP za su tunkari APC tare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel