Budurwa Ta Koka Bayan Mai gidan Da Take Haya Ta Rufe Mata Kofa Kwanaki 4 Da Tarewarta, Bidiyon Ya Yadu

Budurwa Ta Koka Bayan Mai gidan Da Take Haya Ta Rufe Mata Kofa Kwanaki 4 Da Tarewarta, Bidiyon Ya Yadu

  • Da sanyin safiya, wata matashiya yar Najeriya ta koma dakinta na katako kawai sai ta ga cewa mai gidan da take haya ta garkame shi da katon kwado
  • Matashiyar ta yi bidiyon wajen yayin da ta tunkari mai gidan, wacce ke aiki a wata yar gona, don sanin dalilin rufe mata daki
  • Jama'a sun yi martani kan bidiyon inda mutane da dama suka shawarci budurwar kan mataki na gaba da za ta iya dauka

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata budurwa yar Najeriya da ke rayuwa a dakin katako ta koka a soshiyal midiya bayan ta gano cewa mai gidan da take haya ta garkame mata makwancinta.

Da ta garzaya shafin TikTok, ta dauki bidiyoyi kusan guda 10 kan arangamarta da mai gidan da take haya.

Budurwa ta koka bayan mai gidansu ta garkame mata kofa
Budurwa Ta Koka Bayan Mai gidan Da Take Haya Ta Rufe Mata Kofa Kwanaki 4 Da Shigarta Gidan, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @lifeinkpako
Asali: TikTok

A cewar matashiyar, kwanaki hudu kenan da tarewarta a cikin gidan kuma ba tan san laifin da ta aikata ba. Ta ziyarci mai gidan da take haya a gonarta don sanin dalili.

Kara karanta wannan

Saurayi Ya Hana Budurwa Shiga Gidansa Bayan Ta Kai Masa Ziyarar Bazata, Ya Mata Bidiyo

Mai gidan ta ce ana binta kudin wuta

Ga mamakinta, mai gidan hayar mara fara'a ta ce ta rufe mata kofar dakinta ne saboda ana bin ta bashin kudin wuta N1,500.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakan ya ba matashiyar mamaki yayin da take al'ajabin ta yadda mutumin da bai yi ko mako daya a cikin gida ba zai ci bashin wutar lantarki.

Matashiyar ta nuna fushinta cikin sanyi yayin da suke musayar yawu da mai gidan.

Kabbi bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Cuteblezz ta ce:

"Idan har kin san baki yi mata laifi ba ki yi hankali da ita mugwayen mutane a ko'ina idan da hali ki sauya muhalli ki nemi wani gidan sannan ki dage da addu'a."

Nancy Joel ta ce:

"Baaba mutane na da matsala a duniyar nan faa ta ce sau nawa za ki gaishe da ni."

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Kadu Yayin da Ta Isa Wajen Bikin Mijinta, Aminiyarta Ce Amaryar Da Ya Yi

PRECIOUS ta ce:

"Yi hakuri ba wannan kwadon bane kika ce kin siya #1000 kodai idanuna na yaudarata ne?"

Matashi ya siya yar tsana saboda rashin budurwa

A wani labari na daban, wani mutumi ya baje kolin mutum-mutuminsa a soshiyal midiya, yana mai cewa ya siye ta saboda ya gaza samun budurwa mutum.

A wani bidiyon TikTok, mutumin ya fito da mutum-mutuminsa mai tsawon mutum daga cikin kwali sannan ya dungi motsa jikinta da taimakon na'urar da ta zo da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel