Sai Kace a Karkara: Matashi Ya Saki Bidiyon Wani Gida Da Za a Ba Da Haya N650k Duk Shekara a Lagas

Sai Kace a Karkara: Matashi Ya Saki Bidiyon Wani Gida Da Za a Ba Da Haya N650k Duk Shekara a Lagas

  • Wani matashi dan Najeriya ya saki bidiyon ban dariya na wani gida da dillalin gida ya nunawa kawarsa kan kudi N650k
  • Yayin da yake wallafa bidiyon a shafinsa na Twitter, ya bayyana cewa dillalin gidan ya yi bayanin gidan a matsayin na 'ba ruwan wani da wani'
  • A bidiyon, matashiyar da dillalin gidan sun shiga cikin fallen dakin amma yanayin fuskarta ya nuna ba haka ta yi tsammani ba

Wani matashi mai suna @Papijendi a Twitter ya saki wani bidiyo na gidan da wani dillalin gida ya yi ikirarin za a bayar da hayarsa kan N650,000.

An bukaci dillalin gidan ya nemo daki ciki da falo, amma sai ya samo falle daya da bandaki kuma babu madafi.

Gidan haya
Sai Kace a Karkara: Matashi Ya Saki Bidiyon Wani Gida Da Za a Ba Da Haya N650k Duk Shekara a Lagas Hoto: @papijendi
Asali: Twitter

Dillalin gidan ya yi ikirarin cewa za a bayar da hayan dakin ne kan N650,000, lamarin da yasa mutane suka kasa boye kaduwarsu.

Kara karanta wannan

Uwa Ta Fasa Asusun Yaranta Bayan Shekaru 10, Ta Fitar Da Tsoffin Kudi a Bidiyo

A bidiyon, dillalin gidan ya nunawa matashiyar dakin da bandaki a ciki amma babu madafi. Harabar gidan ya yi kaca-kaca kuma ba a yi wa gidan fenti ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An wallafa bidiyon a Twitter dauke da taken:

"Dillalan gidan Lagas ba za su kashe mutum ba...kalli abun da suka nunawa kawata a matsayin ciki da falo (gaba daya kudin haya 650k).

Jama'a sun yi martani

@nancytaiye ta ce:

"Babu ruwan wani da wani ne ko ba shi bane?"

@SayYourMind01ta rubuta:

"Ina uwar daka? ina falo?"

@aridunnu05 ta kara da cewar:

"Dillalin na kuma wage hakora."

@PadrinoDebo ya yi martani:

"Bayan ya fadi 650k hakoransa nawa kuka cire."

Kalli wallafar a kasa:

Ladan haihuwa: Matashi ya gwangwaje iyayensa na sabon gida irin na zamani

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani matashi ya garzaya shafukan soshiyal midiya domin nuna gagarumin kyautar da ya yi wa iyayensa abun kaunarsa duniya da lahira.

Kara karanta wannan

Bidiyon Matashi Tafe da Janaretonsa Har Gidan Mai don Siyan Fetur Cike da Alfahari ya ba Jama'a Dariya

Matashin dai ya ruguza gidan iyayensa a kauye sannan ya dankara masu sabon gini irin na zamani sai kace a birni ga kuma katon 'gate' da katanga a gidan.

Jama'a da dama da suka ci karo da bidiyon sun jinjinawa matashin a kan wannan namijin kokari da ya yi inda wasu suka dungi kwararo masa ruwan addu'o'i.

Asali: Legit.ng

Online view pixel