"Kudin Haya Kawai Na Ke Da Shi": Budurwa Ta Tare a Dakin Da Ta Kama Ba Tare Da Komai Ba, Bidiyon Ya Bazu

"Kudin Haya Kawai Na Ke Da Shi": Budurwa Ta Tare a Dakin Da Ta Kama Ba Tare Da Komai Ba, Bidiyon Ya Bazu

  • Wata budurwa ta tare a sabon gidanta mai daki guda tare da gado kawai tunda abin kadai za ta iya siya kenan
  • Budurwar, mai suna Beaty Nain, ta wallafa bidiyon dakinta a Tik-Tok, tana nuna yadda ya ke wayam sai dai kawai gadonta
  • Beauty ta ce kudin haya kawai ta ke da shi amma bata da kudin siyan kayan daki

Wata budurwa ta wallafa bidiyon gidan da ta kama haya mai daki daya inda ta tare da gado kawai.

Budurwar, @beautynain ta ce ita fa kudin biyan haya kawai ta ke da shi kuma ta biya don haka ba ta da kudin siyan kayan daki.

Yar Tik-Tok
"Kudin Haya Kawai Na Ke Da Shi": Budurwa Ta Tare a Dakin Da Ta Kama Ba Tare Da Komai Ba, Bidiyon Ya Bazu. Hoto: Photo credit: TikTok/@beautynain
Asali: UGC

Bayan ta tare a gidan, yanzu tana neman yadda za a yi ta siya kayan daki da za ta kawata gidan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yadda Wani Matshi Da Yaje Ba Haya A Dawa Karke Da Fada Da Damisa Wadda Ta Jikkatashi

Yarinyar ta koka bayan tarewa a gida ba tare da kayan daki ba

A bidiyon da ta wallafa, an ganta zaune a cikin karamin dakin kan katifarta karami ta yi zugum.

Kuma, ta tafi bandaki ta nuna yadda ya ke da tsafta. Ta kuma shiga kicen ta nuna cupboard dinta.

Ta wallafa bidiyon tana mai cewa:

"Wannan gidan ba zai samar da kayan daki da kansa ba. Kamar wasa na ke yi. Allah ya mana gafara."

An karfafa mata gwiwa cewa a kalla ta iya biyan kudin hayan da kanta.

Kalli bidiyon a kasa:

Masu amfani da TikTok sun yi martani kan dakin mara kaya

@Tamitayo 1136 ya ce:

"Nasara dai nasara ne."

@nazareth19912chizzy ya yi martani:

"Tamkar ni. Na fara siyan kayan gida ne daga wata Fabrairu kuma tun watan Nuwamba na biya kudin haya... abin ba sauki fa."

@thrift by princess ta ce:

"Abin da na ke fama da shi yanzu. Nawa ya fi hakan muni saboda na biya N250k don gida. Yanzu ba za ka iya ganin N1000 ka siya abinci ba."

Kara karanta wannan

Yadda Budurwa Ta Zage Ta Yi Fentin Gidanta Da Kanta Ya Burge Jama'a, Bidiyon Ya Yadu

@Rosey ta ce:

"Nima haka na ke ciki ... kadan-kadan ne."

@simplyblessing05 ya ce:

"Duk za mu kai wurin wata rana."

Wata tsaleliyar budurwa ta fada wa dan acaba 'ina son ka'

A wani rahoton daban, wata budurwa ta janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta na zamani inda ta ke fada masa cewa tana son sa.

Shi kuma dan acaban yana cike da kunya yayin da ta shafa masa kai tana masa magana har ta bashi kyautar N20.

Asali: Legit.ng

Online view pixel