Yadda Abokan Ango Suka Duba Ko Bakinsa Na Wari Kafin Ya Sumbaci Amaryarsa, Bidiyon Ya Ja Hankali

Yadda Abokan Ango Suka Duba Ko Bakinsa Na Wari Kafin Ya Sumbaci Amaryarsa, Bidiyon Ya Ja Hankali

  • Wani bidiyo da ke nuna lokacin da wasu abokan ango ke shirya abokinsu kafin ya sumbaci matarsa ya haddasa cece-kuce
  • Gaba daya abokan sun nishadantar da mahalarta bikin yayin da suka yi masa gyaran fuska, suka goge masa fuska, suka ba shi turaren jiki, sannan ma suka duba bakinsa ko yana wari
  • Yan Najeriya da suka yi martani ga bidiyon ma'auratan sun yi barkwanci cewa da su ne amaryar da sun sumbaci wani daban

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani mutumi ya nuna yar dirama da abokansa suka shirya a lokacin da zai sumbaci amaryarsa a ranar aurensu.

Yayin da shi (@y0ung.15) ya bude fuskar matar, sai daya daga cikin abokansa ya yi masa gyaran fuska. Wani abokin ango kuma ya duba ko yana kamshi kafin ya ba shi turaren jiki ya fesa.

Kara karanta wannan

“Albashina Na Farko a Canada”: Matashi Dan Najeriya Da Ya Koma Turai Da Zama Ya Siya Hadaddiyar Mota

Abokan ango na duba bakinsa
Yadda Abokan Ango Suka Duba Ko Bakinsa Na Wari Kafin Ya Sumbaci Amaryarsa, Bidiyon Ya Ja Hankali Hoto: @y0ung.15
Asali: TikTok

Abokan ango sun nishadantar da mahalarta biki

Mahalarta bikin sun nishadantu da wannan yar dirama da abokan angon suka shirya. A kusan karshen bidiyon, wani mutum ya zo ya duba bakinsa ko yana wari.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da ya lura cewa yana wari, sai ya ba shi yar minti mai kawar da warin baki. Matar tana ta kallon abokan angon nata yayin da ta ci gaba da dariya.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama'a

Favor ta ce:

"Na yi dariya lokacin da ya bude bakinsa....Ina taya ma'auratan murna."

Ferthanys_beautyspot ta ce:

"Amfanin abokai kenan don taya murna."

user4916129420917 ya ce:

"Ina taya ku murna, ina maku fatan alkhairi a gidan aurenku."

teez_dora ta ce:

"Da na aure wani daban kawai, kada ku bata mani lokacina."

iamkpakpandobackup ta ce:

"Yarinyar na fadi a ranta 'yallabai ka zo ka sumabaceni faah."

Kara karanta wannan

Ma’aikacin Banki Ya Bayyana Yadda Ya Yi Amfani Da PoS Da Aka Yi Kutse Wajen Cire Kudi Sau 5 Daga ATM Din Kwastoma

that_girl_ucheta ce:

"Gaba daya abun da kake bukata a duniyar nan shine yan uwa da abokan arziki...duniyar na iya zama wajen jin dadi."

Yan mata 3 da suka fita daga ciki daya sun zama matukan jirgin sama, hotonsu ya yadu

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu yan mata yan Najeriya uku da suka fito daga jihar Ondo wadanda iyayensu daya sun zama matukan jirgin sama.

Wani mai amfani da Twitter Oluyemi Fasipe ne ya wallafa hoton yan matan kuma tuni ya yadu tare da haifar da martani masu dadi daga bangarori daban-daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel