"Na Tausaya Mata": Matar Aure Ta Je Wurin Biki Ta Tarar Babbar Kawarta Mijinta Yake Aure

"Na Tausaya Mata": Matar Aure Ta Je Wurin Biki Ta Tarar Babbar Kawarta Mijinta Yake Aure

  • Wani bidiyo ya nuna yadda aka yi wata dirama a wajen wani ɗaurin aure bayan matar aure ta gano amaryar babbar ƙawarta ce
  • Ta ƙalubalanci amaryar cikin ƙunar rai da bacin rai a cikin muryarta sannan ta hana mijinta ya taɓa ta
  • An bayyana mabambantan ra'ayoyi kan bidiyon yayin da mutane su ke maganar yadda amana ta yi wahala sosai a yanzu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

An samu wata ƴar hatsaniya a wajen wani ɗaurin aure bayan matar aure ta gano cewa mijinta babbar ƙawarta yake shirin aure.

Bidiyon lamarin wanda aka sanya a soshiyal midiya, ya nuna matar na ƙalubalantar babbar ƙawarta cikin raɗaɗin jin zafin cin amanar da ta yi mata.

Matar aure ta gano babbar kawarta na aure mata miji
Matar auren ta harzuka matuka Hoto: @remedyblog
Asali: Instagram

Wani mai amfani da sunan @priestagramm a Instagram, wanda ya yi martani kan bidiyon, ya fassara ɓaɓatun da matar take yi wanda a cewarsa cikin yaren Wolof ne, wani yare a ƙasar Senegal ko Gambia.

Kara karanta wannan

Kyakkyawan Kurma Ya Koka Kan Rashin Samun Budurwa, Ya Ce 'Yan Mata Sun Ki Yarda Su Yi Soyayya Da Shi

A cewarsa, matar ta zargi babbar ƙawarta da zama babbar munafuka inda tace mata idan ta isa ta ɗago ido ta kalleta ta tabbatar mata da cewa lallai za ta aure mata miji.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga nan sai matar auren ta gaya wa mijinta, wato angon cewa ba za ta yi masa magana ba.

Fassarar da @priestagramm ya yi na cewa:

"Dukkanin ku munafukai ne. Ka da wanda ya taɓa ni.... Nabou ke ce babbar munafukar a cikinsu... Ni za ki yi wa haka? Kin kasance babbar ƙawata. Ki kalli tsabar ido na ki gaya min cewa ni za ki yi wa haka. Kafin ta gaya wa mijinta cewa ba da shi take magana ba. Suna magana ne da yaren Wolof, wani yare na ƙasashen Senegal da Gambia."

Kara karanta wannan

Cire Tallafin Man Fetur: Gwamnan Jihar Arewa Ya Kaddamar Da Rabon Tallafi Ga Mutum 1.8m

Ƴan soshiyal midiya sun yi martani

omabarbie1 ta rubuta:

"Yanzu ƙawaye ne ke cin amana shiyasa ya fi kyau ka da mutum ya tara su. Na ji a jika a hannun ƙawaye, har yanzu ma ina ji."

simbistar100 ya rubuta:

"Yadda matar ta yi wa mijinta ya nuna irin raɗaɗin da take ji. Mata su ma suna da haƙƙi, don haka kafin ka cutar da wani ka tsaya ka tambayi kan ka idan aka yi maka haka za ka ji?"

sheischidubem ta rubuta:

"Yakamata mata su saba da barin ƙawaye ko wani wanda yake son abinda su ke da shi, za ta iya kasancewa ta ƙwarai amma wannan ɗabi'ar babbar barazana ce."

sommie_d_great ta rubuta:

"Irin waɗannan mazajen suna cutar da mata masu kirki suna ɗaukar su kamar ba su da zuciya, su kuma dawo suna cewa ba su ga matan ƙwarai ba. Namiji ɗan Afirika ba zai taɓa yarda a yi masa kishiya ba, amma zai tilasta mace ta zauna da babbar ƙawarta a matsayin kishiya."

Kara karanta wannan

Tsadar Mai: IPMAN Ta Koka, Ta Bayyana Yadda 'Yan Kasuwar Man Fetur Ke Ji a Jika a Dalilin Cire Tallafi

Matar Aure Ta Koka Kan Auren Babbar Kawarta Da Mijinta Zai Yi

A wani labarin da Legi.ng ta kawo a baya, kun ji cewa wata matar aure ta koka bayan mijinta zai yi mata kishiya.

Matar auren wacce ƴaƴanta uku tare da mijinta ta koka kan cewa da babbar ƙawarta zai yi mata kishiya bayan ya gama cin moriyarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel