‘Ni Ba Barawo Ba Ne’: Sanata Kalu Ya Zubar da Kwalla a Majalisa Saboda Abin da Ya Faru Dashi a Magarkama

‘Ni Ba Barawo Ba Ne’: Sanata Kalu Ya Zubar da Kwalla a Majalisa Saboda Abin da Ya Faru Dashi a Magarkama

  • Sanata Orji Kalu ya bayyana cewa, shi ba barawo bane, kuma sam bai taba sata ba amma aka kakaba masa sata
  • Ya ce kafin ya shiga siyasa ma yana da kudinsa, kuma ya yi tasiri wajen kafa jam’iyyar PDP mai adawa a kasar
  • Ya zuwa yanzu, ya shafe shekaru hudu a majalisar dattawa, inda ya godewa abokan aikinsa bisa ba shi goyon baya

FCT, Abuja - Sanata Orji Uzor Kalu ya zubar da kwalla a zauren majalisar dattijai ta tara a ranar Asabar yayin da ya bayyana cewa shi "ba barawo ba ne", Daily Trust ta ruwaito.

Hukumar da ke yaki da rashawa ta EFCC, ta gurfanar da tsohon gwamnan Abia da Ude Jones Udeogu, tsohon daraktan kudi kuma akantan jihar a gaban kuliya bisa zarge-zarge 36 na karkatar da kudaden da suka kai N7.1bn.

Kara karanta wannan

Ga irinta nan: Yadda aka yiwa masu kwacen waya 2 a Kano hukunci mai tsanani a kotun Muslunci

A ranar 5 ga Disamban 2019, an yankewa Kalu hukuncin daurin shekaru 12 a gidan yari, yayin da Udeogu ya samu hukuncin shekaru 10 a magarkama.

Orji Kalu ya tuna baya, ya sharbi kuka
Sanata Orji Uzor Kalu kenan | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Yadda Kalu ya tsira

Daga baya kotun kolin kasa ta soke hukuncin da aka yankewa Kalu da wanda ake tuhumarsa tare dashi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kotun kolin ta ce Mohammed Idris, alkalin kotun da a lokacin aka karawa girma zuwa kotun daukaka kara, bai kamata ya jagoranci shari’ar ba.

Daga wancan lokacin, babu wata sabuwar tuhuma da aka saka kakabawa a kansa, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.

Ni mai kudi nem ba barawo bane ni, cewar Kalu

Kalu ya ce kafin ya tsunduma harkokin siyasa, ya kasance mai tarin arziki kuma ya yi tashe ainun ta fuskar kudi wajen kafa jam’iyyar PDP.

Da yake jawabi cikin kwalla, ya ce:

Kara karanta wannan

Tsadar Mai: Magidanci Da Matarsa Ta Yi Kararsa Ya Ki Halartar Zaman Kotu Saboda Kudin Mota a Kaduna

“Kafin ma na shigo siyasa, zan iya siyan duk wani abu da kudi zai iya saye. Ni ba barawo bane.
“Wadanda suka jefa ni a gidan yari sun san dalili. Sun kwace kasuwancina kuma sun so su kashe ni amma duk da haka na tsira kuma yanzu nake cikin majalisar dattawa tare da ku.
“Ban taba rashi ba. A lokacin da nake jam’iyyar PDP inda na yi wa’adi biyu a matsayin gwamna, ni na kawo kudin da suka yi amfani da su wajen kafa waccar jam’iyyar, duk wani kwabo a 1997 da 1998, amma daga baya na zama barawo.
“Mutanen da na ba da kudin sufuri daga gidana a VI sun zama wakilai. Wannan shi ne yadda Najeriya take. Na gode da kuka ba ni wadannan shekaru hudu na goyon baya mara yankewa.”

Kalu na daga masu neman shugabancin majalisa

A bangare guda, Kalu ya bayyana burinsa na zama shugaban majalisar dattawa ta 10 tun bayan da aka kammala zaben bana.

Kara karanta wannan

Cire Tallafin Mai: Dole A Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, TUC Ta Fadi Bukatunta

Sai dai, ya samu koma baya yayin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana rashin goyon bayansa.

Abdulaziz Yari na daga cikin wadanda ke neman kujerar mai daraja ta biyu a Najeriya, amma har yanzu ba a kammala batun ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel