Tsadar Mai: Magidanci Da Matarsa Ta Yi Kararsa Ya Ki Halartar Zaman Kotu Saboda Kudin Mota a Kaduna

Tsadar Mai: Magidanci Da Matarsa Ta Yi Kararsa Ya Ki Halartar Zaman Kotu Saboda Kudin Mota a Kaduna

  • Kotun da ke zamanta a Kaduna ta gurfanar da wani mutum a gaban kotu a ranar Laraba 7 ga watan Mayu
  • Wanda ake zargin Ali Abubakar bai samu halartar zaman kotun ba saboda dalilin rashin kudin mota
  • Kotun ta bukaci a kira shi a waya tun da yana Abuja don neman martaninsa akan tuhumarsa da ake

Jihar Kaduna – Wani mutum mai suna Ali Abubakar da matarshi, Ajinomo Ohunenene-Ummi ta maka shi a kotu ya ki halartar zaman kotun saboda rashin kudin mota.

Kotun wadda ke zamanta a Kaduna ta tura sako zuwa ga Ali Abubakar ta hannun masinjanta Tajudden Saidu.

Wani da ake zargi ya ki halartar zaman kotu saboda rashin kudin mota
Kotu a Najeriya. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Ali ya ce ba zai samu halartar zaman kotun ba saboda rashin kudin mota daga Abuja zuwa Kaduna, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Binciken Majalisa Ya Tsumbula Gwamnatin Buhari a Badakalar Naira Biliyan 910

Ya bukaci kotun ta yi duk abinda ya dace

Ya roki kotun da ta ci gaba sauraran karar da kuma bai wa wadda take karar abin da take so.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tun farko, wadda ke karar ta bakin lauyarta, Nafisa Ibrahim ta ce tana son samun ‘yanci a auren kuma za ta iya dawo da sadakin N50,500 ga mijin nata.

Ta roki kotu da ta ba ta damar kulawa da ‘yarsu mai shekara guda a duniya, inda kuma ta roki kotun da ta umarci mijin ya rinka ba ta N20,000 duk wata don ciyar da ‘yar tasu.

Alkalin kotun ya bukaci a kira wanda ake zargin a waya

Mai Shari’a, Mallam Abdulrahman Isiyaku ya umarci masinjan kotun da wadda ke karar su kira Abubakar a waya don mai da martani akan tuhumarsa da ake.

Masinjan kotun ya fada wa kotu cewar Abubakar ya yadda zai sake matar, amma N10,000 kawai zai iya biya don ciyar da ‘yar tasu.

Kara karanta wannan

Cire Tallafin Mai: Dole A Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, TUC Ta Fadi Bukatunta

Ya kara da cewa Abubakar ya ce matar ta yi amfani da kudin sadakin don ciyar da ‘yar na watanni biyar, Daily Post ta tattaro.

Mai Shari’a ya tambayi matar idan ta amince da hakan, yayin da ta ce ta amince da butar tasa.

Daga nan ne Alkalin kotun ya raba auren tare da umartan matar ta rike N50,500 don ciyar da ýarinyar har tsawon watanni biyar.

Ya kuma umarci wanda ake zargin da ya ci gaba da kula da lafiya da tufafi da kuma ilimin yarinyar har zuwa lokacin da za ta girma.

Ina Matukar Son Matata: Fasto Ya Roki Alkali Kada Ya Raba Aurensu

A wani labarin, Wani Fasto mai suna Omoha Lucky ya roki kotun da ke zamanta a Nyanya a Abuja da kada ta raba aurensa da matarsa.

Faston ya bayyana cewa yana matukar son matarsa kuma bai shirya zama babu ita ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel