Majalisa Ta 10: Yari Da Kalu Sun Samu Koma Baya, Tsohon Shugaba Buhari Ya Watsa Musu Kasa a Ido

Majalisa Ta 10: Yari Da Kalu Sun Samu Koma Baya, Tsohon Shugaba Buhari Ya Watsa Musu Kasa a Ido

  • Sanata Godswill Akpabio na ƙara samun tagomashi a ƙoƙarin da ya ke yi na zama shugaban majalisar dattawa ta 10
  • Ƙoƙarin da wasu daga cikin yan takarar suka yi na samun goyon bayan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, bai haifar da ɗa mai ido ba
  • Buhari ya buƙace su da su daina kamun ƙafar da suke yi su aminta da abinda jam'iyya ta yanke kan shugabancin majalisar

Katsina, Daura - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi fatali da neman shugabancin majalisar dattawa na Sanata Orji Uzor Kalu da Sanata Abdulaziz Yari.

A cewar wani majiya wanda ya bayar da bayanin abinda ya faru bayan Yari ya ziyarci Buhari, tsohon shugaban ƙasar ya fito ƙiri-ƙiri ya yi fatali da buƙatarsa inda ya ƙi nuna goyon bayansa a gare shi.

Kara karanta wannan

PDP, Labour Party Sun Taso Shugaba Tinubu a Gaba Bisa Jan Kafa Wajen Bayyana Kadarorinsa

Shugaba Buhari ya yi fatali da bukatar Yari Kalu
Tsohon shugaban ƙasar ya bukaci su mutunta matsayar jam'iyya Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Majiyar ya nuna cewa shugaba Buhari bai ji daɗin yadda Yari ya ke neman shugabancin majalisar dattawan ba, cewar rahoton Vanguard.

"Sun zo Daura suna tunanin cewa Aza su yi amfani da kuɗi domin siye uwargidan tsohon shugaban ƙasa, saboda sun yarda cewa kuɗi za su iya sanya wa su samu wannan muƙamin." A cewar majiyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An gaya musu su koma su mutunta zaɓin da shugaban ƙasa da jam'iyya suka yi akan shugabancin majalisar. "

Buhari sai da ya gargaɗi Yari kan bijirewa matsayar jam'iyyar saboda cikar wani buri nasa na ƙashin kansa.

Aisha Buhari ta ƙi yarda ta taimakawa Yari

Haka kuma ƙoƙarin da suka yi na ganin Aisha Buhari ta sanya baki saboda Yari, shi ma ya ci tura.

Aisha ta buƙaci Yari da ya mayar da hankali wajen ganin an samu haɗin kai a ƙasa, saboda muhimmancin da hakan ya ke da shi.

Kara karanta wannan

Kalubale 10 Masu Hadari Da Tinubu Ya Tsallake Kafin Shiga Fadar Shugaban Kasa

Rahotanni sun tabbatar da cewa Yari ya samu rakiyar zaɓaɓɓun sanatoci guda biyar, a ziyarar da ya kai Daura wajen tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Yan Majalisu Ke Raba Daloli Don Neman Goyon Bayan a Zabe Su

A wani rahoton na daban kuma, wasu daga manyan ƴan takarar shugabancin majalisa ta 10 sun fara rabon daloli domin samun goyon baya.

Ƴan takarar dai na neman shugabancin majalisar ko ta halin ƙaƙa domin gadar Ahmed Lawan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel