Kamar Kullum: Saudiyya Ta Ba Wa Najeriya Kyautar Dabino Tan 50 Don Raba Wa 'Yan Kasa

Kamar Kullum: Saudiyya Ta Ba Wa Najeriya Kyautar Dabino Tan 50 Don Raba Wa 'Yan Kasa

  • Kasar Saudiyya ta bai wa kasar Najeriya kyautar dabino har tan 50 don habaka hulda tsakaninsu
  • Jakadan kasar a Najeriya, Faisal Alghamdi shi ya ba da kyautar a madadin kasar Saudiyya a Abuja
  • Kyautar an ba da ita ne ta hannun daraktan yanki a ma'aikatar kasashen waje, Janet Osita a Abuja

FCT, Abuja - Kasar Saudiyya ta gabatar da kyautar tan 50 na dabino mai inganci ga kasar Najeriya don kara habaka hulda tsakanin kasashen biyu.

Jakadan kasar Saudiyya a Najeriya, Faisal Alghamdi shi ya ba da kyautar a madadin kasar Saudiyya a yayin wani biki a Abuja.

Saudiyya ta bai wa Najeriya kyautar dabino
Kasar Saudiyya Ta Bai Wa Najeriya Kyautar Dabino. Hoto: Peoples Gazette.
Asali: Facebook

Da yake mika kyautar, shugaban tawagar KSRelief, Nezat Talaqi ya ce kyautar daga mai kula da masallatai masu tsarki guda biyu na Sarki Salman Al Saud ne.

Ya bayyana irin taimakon da suke bai wa Najeriya

Kara karanta wannan

Binciken Majalisa Ya Tsumbula Gwamnatin Buhari a Badakalar Naira Biliyan 910

Ya ce gwamnatin kasar Saudiyya karkashin hukumar tallafi da agaji ta KSRelief tana ba da tallafi ga gwamnatin Najeriya, cewar Daily Nigerian.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa taimakon kwanan nan da hukumar ta yi shi ne bai wa mutane 48,300 Kwando cike da abinci a jihohin Kano da Yobe da kuma Borno akan kudi $500,000, cewar rahotanni.

A cewarsa:

“Ba da wadannan dabinai na daga cikin tallafi da kuma taimako daga mai kula da masallatai masu tsarki guda biyu, Allah ya kare shi.
“Muna ba da taimakon ga kasashen da muke da kyakkyawan alaka da su wandanda Najeriya ke ciki don mutane masu bukata.
“Wadannan da wasu yana tabbatar da yadda kasar Saudiyya ke kara inganta mu’amala tsakaninsu da Najeriya a dukkan matakai.
”Sannan za mu ba da magani kyauta ga ýan Najeriya nan ba da jimawa ba a jihohin Kano da Lagos da sauransu.

Kara karanta wannan

An Shirya Tsaf, 'Yan Kwadago Sun Janye Yajin-Aiki Bayan An Yi Kus-Kus a Aso Rock

Janet Olisa ta karbi kayan tare da godiya

Da take karban kayan, daraktan yanki a ma’aikatar kasashen waje, Janet Olisa ta godewa kasar Saudiyya inda ta ce ‘yan Najeriya na godiya matuka da wannan kyauta.

A cewarta:

“Ko wace shekara, gwamnatin Saudiyya suna taimaka wa Najeriya da dabino, yau sun kawo, muna godiya sosai akan abin da suke yi kullum.

Alhazan Birnin Tarayya Abuja Na Cikin Tsaka Mai Wuya a Saudiyya

A wani labarin, mahajjata daga birnin tarayya Abuja suna shan bakar wahala a kasa mai tsarki saboda rashin kyawun matsuguni.

Alhazan suna can sun yi cirko-cirko saboda karancin mazauni, matsalar wadda ake ganin daga mahukunta ne saboda rashin tsari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel