Alhazan Birnin Tarayya Abuja Na Cikin Tsaka Mai Wuya a Saudiyya

Alhazan Birnin Tarayya Abuja Na Cikin Tsaka Mai Wuya a Saudiyya

  • Mahajjatan bana na birnin tarayya Abuja sun tsinci kansu cikin halin ƙaƙanikayi a ƙasa mai tsarki ta Saudiyya
  • Mahajjatan sun rasa matsuguni a ƙasa mai tsarki saboda rashin yi musu tanadin waje mai kyau da za su zauna
  • An yi zargin cewa hakan ya faru ne saboda ƙara yawan kujerun da aka ware wa Abuja da wasu shafaffu da mai suka yi

Saudiyya - Alhazan babban birnin tarayya Abuja, na shan baƙar wahala a ƙasa mai tsarki bisa rashin yin tsari mai kyau na inda za su zauna a Saudiyya.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa wasu daga cikin mahajjatan farko da suka isa ƙasa mai tsarki, na can sun yi cirko-cirko saboda mazauninsu bai cika ƙarancin abinda kwamitin shirye-shirye na aikin Hajji ya gindaya ba.

Kara karanta wannan

Yana Dab Da Sauka Mulki, Shugaba Buhari Ya Bayyana Wani Abu Da Ya Faru Da Shi Wanda Bai Taba Tunani Ba

Alhazan birnin tarayya Abuja sun makale a Saudiyya
Wasu daga cikin Alhazan Najeriya (Ba wadanda lamarin ya ritsa da su ba) Hoto: Hajjreporters.com
Asali: UGC

Wata majiya mai ƙarfi ta bayyana cewa shugaban hukumar jindaɗin Alhazai ta birnin tarayya Abuja, Malam Abubakar Evuti, ya nuna sakaci sosai da rashin ƙwarewa kan aikinsa.

Hukumar Alhazai ta ƙasa ta ware kujeru 3, 562 ga birnin tarayya Abuja, yayin da hukumar jindaɗin Alhazan ta Abuja ta ƙara yawansu ya kai fiye da kujeru 4,000, cewar rahoton New Telegraph.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ƴan siyasa sun ƙara taɓarɓara lamura

Wani jami'in hukumar wanda ya nemi da a sakaya sunansa, ya bayyana cewa tsohuwar ƙaramar ministar birnin tarayya Abuja, ta ƙara taɓarɓara lamarin inda ta karɓe kujeru da dama.

An kuma bayyana cewa tsohuwar ƙaramar ministan ta bayar da kujerun ne ga ƴan siyasa na kusa da shugaba Tinubu, domin yin kamun ƙafa a sake mayar da ita kan muƙaminta.

Ɗaya daga cikin mahajjatan wanda ya nemi da kada a bayyana sunansa, ya koka kan yadda su ke shan wahala, inda ya ce da yawa daga cikinsu sun fara cire ɗokin da su ke kan aikin Hajjin.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Ba Bola Tinubu Muhimmiyar Shawara Mai Ratsa Jiki Ana Dab Da Rantsar Da Shi

Har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, ofishin watsa labarai na hukumar bai ce komai ba dangane da lamarin.

Jirgin Mahajjata Daga Jigawa Ya Yi Saukar Gaggawa a Kano

A wani labarin na daban kuma, wasu mahajjata daga jihar Jigawa sun tsallake rijiya da baya bayan jirginsu ya yi saukar gaggawa a jihar Kano.

Jirgin ya sauka a Kano ne sakamakon ruwan sama wanda ya so ya yi ɓarnata wani sashin jirgin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel