Muna Neman Kari: Arewa Ta Tsakiya Ta Ce Nada SGF Bai Wadatar Ba, a Sake Duba Lamarin

Muna Neman Kari: Arewa Ta Tsakiya Ta Ce Nada SGF Bai Wadatar Ba, a Sake Duba Lamarin

  • Kungiyar NCPF ta bukaci Shugaba Tinubu da ya nada dan yankin Arewa ta Tsakiya a mataimakin shugaban majalisar dattawa
  • Kungiyar ta ce zaban George Akume bai kai ya saka musu ba ganin yadda suka bai wa Tunbu kuri’u a zaben da aka gudanar
  • Sannan sun bukaci ya dauko ministan birnin Tarayya Abuja daga yankin Arewa ta Tsakiya kamar yadda aka yi a baya

FCT, Abuja – Kungiyar Arewa ta Tsakiya ‘North Central People’s Forum’ ta ce ba ta gamsu da zaban dan yankin ba a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya da Bola Tinubu ya yi ba.

Kungiyar ta ce zaban George Akume kadai bai wadatar ba, ya kamata a ba su mataimakain shugaban majalisar dattawa kuma dan asalin birnin Tarayya Abuja shi ya kamata a bai wa ministan Abuja.

Bola Tinubu
NCPF Ta Ce Nada SGF Bai Wadatar Ba, a Sake Duba Lamarin. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Sakataren hulda da jama’a na kungiyar, Honarabul Audu Sule shi ya bayyana haka a wata sanarwa, inda ya ce ganin yadda yankin ya bai wa Tinubu kuri’u masu yawa, ya kamata ya samu ministan Abuja da kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Sun bukaci nada ministan Abuja daga yankinsu

Ya ce mutanen yankin da suka hada da Abuja da Plateau da Benue da Kogi da Niger da kuma Nasarawa sun sani cewa ya kamata wani daga wadannan jihohi ya zamo ministan Abuja, cewar Vanguard.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Idan ba a manta ba, Shugaba Tinubu ya nada George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya don ya dadadawa ‘yan yankin wanda suka rasa duk wasu mukamai a majilisun tarayya.

Kungiyar ta ce hakan ba zai sa su ji an yi abin da ya dace ba, inda suka ce Sanata Sani Musa daga jihar Niger da Idris Wase daga Plateau duk sun nemi takarar a majalisun tarayya a kujeru daban-daban amma a banza.

Kungiyar ta ce an nada Akume don rufe musu baki

Sanarwar ta kara da cewa, zaban Akume an yi shi ne don bai wa Abbas daga Arewa maso Yamma damar zama kakakin majalisa, cewar rahotanni.

Audu ya ce:

“Mai girma shugaban kasa, mun gode da nada dan mu kuma uba sannan kuma dan uwa a matsayin SGF, zamu yi amfani da wannan dama don taya shi murna saboda ya cancanta.
“Amma hakan bai isa ba, idan ka duba yadda muka baka kuri’u masu yawa a wannan yankin, mun fi ko wace jiha kawo kuri’u idan aka cire jihar Plateau da Abuja da suka zabi jam’iyyar Labour.
“Muna bukatan ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawa a wannan yanki, wannan shi ne ofishin da bamu taba samu ba, a baya an nada dan wannan yanki a matsayin ministan Abuja, abin da muke so a wannan gwamnati kenan.”

Shugaba Bola Tinubu Ya Nada Tsohon Ministan Buhari Matsayin SGF

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya nada tsohon ministan ayyuka na musamman, George Akume a matsayin Sakataren Gwamantin Tarayya.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a 2 ga watan Yuni tare da nadin Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma'aikatansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel