Jagora a Jam’iyyar APC Ta Jero Abubuwan da Za Su Taimakawa Tinubu a Mulkinsa

Jagora a Jam’iyyar APC Ta Jero Abubuwan da Za Su Taimakawa Tinubu a Mulkinsa

  • Adaku Ogbu-Aguocha ta na sa ran a gamu da cigaba da nasarori ta kowane bangare a gwamnatin nan
  • ‘Yar siyasar ta ce Bola Ahmed Tinubu zai gyara kasar nan domin da shirinsa ya hau kan karagar mulki
  • Ganin yadda ya yi mulki a Legas, Ogbu-Aguocha ta ce shugaban kasar ya na da kwarewar da ake bukata

Abuja - Adaku Ogbu-Aguocha wanda jigo ce a jam’iyyar APC a jihar Enugu, ta taya Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima murnar shiga ofis.

A ranar Talata Vanguard ta rahoto ‘yar takarar Sanatar ta Gabashin Enugu ta na yi wa mutanen kasar nan albishir da zuwan shugaba Bola Tinubu.

Adaku Ogbu-Aguocha ta ce mulkin Bola Ahmed Tinubu zai zo da alheri ga duka ‘yan Najeriya domin sabon shugaban kasar ya zo ne da shirinsa.

Kara karanta wannan

“Sai An Tauna Tsakuwa Idan Za a Kai Najeriya Gaba”: Wike Ya Goyi Bayan Tinubu Kan Cire Tallafin Mai

Tinubu
Ana rantsar da Bola Tinubu Hoto: @Buhari Sallau
Asali: Facebook

‘Yar siyasar ta roki jama’a su ba sabon shugaban na Najeriya goyon bayan da yake bukata domin ya samu nasara wajen kawo alherai da cigaban kasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jawabin Adaku Ogbu-Aguocha

"Shugaba Bola Tinubu ya dauki fiye da shekaru goma ya na shiryawa kujerar nan, don haka me zai hana shi samun nasara?
Ya nuna zai iya a lokacin da ya rike Gwamna a jihar Legas, a cikin shekaru takwas ya kawowa jihar cigaba, tayi nisa sosai.
Mun kagara ganin mulki da zai zo da nasarori ta ko ina, tare da fatan Tinubu zai iya amfani da iya jagorancinsa wajen hada-kai.

- Adaku Ogbu-Aguocha

An rahoto ‘yar takarar ta na cewa shugaban kasar ya zo ne da shirinsa, ta ce su na sa ran Gwamnatin Tinubu ba za ta nuna bambancin kabilanci ko addini ba.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Fara Mulki da Ciwon Kai, ‘Yan Kwadago Sun Sa Ranar Shiga Yajin-Aiki

Har jawabin da shugaban kasar ya yi a wajen rantsar da shi sai da ya samu yabon ta.

A kula da mata da matasa

A matsayinta ta mace, Misis Ogbu-Aguocha tayi kira ga sabon shugaban kasar ya ba mata da matasa kulawa ta musamman domin kowa ya amfana.

Mata, matasa da yara ne ginshikin kowace al’umma, jagorar ta APC a yankin Kudu maso gabashin Najeriya, cigabansu tamkar cigaban daukacin kasa ne.

PGF ta na tare da Abbas

Rahoto ya zo cewa Hope Uzodinma ya hadu da ‘yan majalisar da ke goyon bayan takarar Tajuddeen Abbas da Benjamin Kalu, ya ce yana tare da su.

Shugaban kungiyar Gwamnonin na APC ya na ganin APC ta dauko mutanen da suka fi cancanta da jagorantar majalisar wakilan tarayya zuwa 2027.

Asali: Legit.ng

Online view pixel