Jerin Kungiyoyin Ma’aikata 9 Da Za Su Shiga Gagarumin Yajin-Aikin Da NLC Za Ta Shirya

Jerin Kungiyoyin Ma’aikata 9 Da Za Su Shiga Gagarumin Yajin-Aikin Da NLC Za Ta Shirya

  • Kungiyoyin ma’aikata da-dama sun shirya tafiya yajin-aiki a Najeriya a dalilin janye tallafin man fetur
  • Daga cikin kungiyoyin da za su bi NLC zuwa wannan yajin-aiki akwai ‘yan jarida da kuma malaman jinya
  • Sanarwa ta na fitowa daga shugabannin kwadago cewa daga tsakar daren Laraba za a janye aiki a kasar

Abuja - Rahoton nan ya tattaro maku jerin wasu daga cikin kungiyoyin ma’aikatan da aka samu labarin za su shiga yajin-aikin ranar Laraba.

Kungiyar NLC ta tabbatar da wannan matsaya a shafinta na Twitter yayin da ake kammala shirye-shiryen yi wa sabuwar gwamnati bore.

'Yan kwadago sun fusata a dalilin tsadar da litar man fetur ya yi saboda cire tallafi.

Kungiyoyin Ma’aikatan Najeriya Za Su Yi Yajin Aiki
'Yan kwadago a zanga-zanga Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

1. NANNM

Kungiyar NANNM ta malaman jinya da ungonzoma ta fitar da sanarwa ta bakin Elder Otaru Daniel Shuaib a ranar Lahadi cewa za ta shiga yajin-aikin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Elder Shuaib ya fitar da sanarwa daga sakatariyar kungiyar da ke unguwar Garki a Abuja. Sahara Reporters ta ce NANNM da wasu kungiyoyi za su yi yajin.

2. MWUN

Haka zalika babban kwamitin kungiyar ma’aikatan ruwa na MWUN ta bakin Kwamred Erazua Oniha ta shaida cewa su na tare da kungiyar NLC ta kasa.

Kungiyar ta umarci shugabanni, ‘yan kwamiti, da sauran ‘ya ‘yanta da ke tashohin ruwa su shirya.

3. NUJ

Babban sakataren kungiyar NUJ na kasa, Shuaibu Usman Leman ya bayyana cewa ‘yan jaridan Najeriya su na goyon bayan yin yajin-aiki kan cire tallafin fetur.

4. NULGE

Kwamred Isah Gambo wanda shi ne Sakatare Janar na NULGE ta ma’aikatan kananan hukumomi ya fitar da sanarwa, ya ce ‘yan kungiyarsa su yi biyayya ga NLC.

5. NASU

Legit.ng Hausa ta fahimci NASU ta ma’aikatan kwalejin ilmi da sauran makamantan makarantu za ta shiga yajin-aikin ranar Laraba tare da sauran ‘yan kwadago.

Prince Peters Adeyemi JP ya sanar da kungiyarsa wannan matsaya da aka dauka a jiya.

6. SSCUCOEN

Tun a ranar Juma’ar da ta wuce, manyan ma’aikatan kwalejojin ilmin kasar nan su ka tabbatar da cewa da su za a shiga yajin-aikin saboda tashin farashin fetur.

7. NUCECFWW

Tribune ta ce kungiyar nan ta kafintoci watau NUCECFWW wanda aka kafa a 1996, sakatarenta, Ibrahim A. Walama ya ce ba za a bar su a baya a yajin-aikin ba.

8. JUSUN

A jawabin da M. J Akwashiki ya fitar a madadin JUSUN, ya tabbatar da ma’aikatan shari’a za su dakatar da zuwa kotu saboda yajin-aikin da NLC ta kira.

9. NUEE

An ji labari NUEE ta ce janye tallafin fetur ya jawo karin tsadar kaya da wahala ga ‘yan kasa don haka za su tafi yajin-aiki daga karfe 12: 00 na daren Laraba.

Kungiyar NLC ta ‘yan kwadago za ta shirya yajin-aikin ne saboda tashin farashin fetur ba tare da gwamnati ta fito da tsare-tsaren da za su rage radadi ba.

Tattaunawa da Gwamnati

Rahoto ya zo cewa kungiyoyin TUC da NLC za su cigaba da tattaunawa da Bola Tinubu har a warware sabanin da aka samu a dalilin tashin farashin mai.

Shugaban ma’aikatan fadar gwamnati ya ce za a kafa kwamitin hadaka da zai duba karin albashin da za ayi wa ma'aikata domin a rage radadin da aka shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel