Bayanai Sun Bullo Kan Sa Labulen Tinubu da Gwamnonin da Suka Yaki Atiku a PDP

Bayanai Sun Bullo Kan Sa Labulen Tinubu da Gwamnonin da Suka Yaki Atiku a PDP

  • ‘Yan kungiyar G5 da suka yaki Atiku Abubakar a jam’iyyar PDP sun sa labule da Bola Tinubu
  • Seyi Makinde ya shaidawa Duniya dalilinsu na yin kus-kus da sabon shugaban kasar a Aso Rock
  • Gwamnan jihar Oyo ya nuna cewa ko nan gaba jagororin na PDP za su sake yin zama da Tinubu

Abuja - ‘Yan kungiyar G5 a jam’iyyar PDP wanda su ka kira kan su da ‘yan kungiyar Integrity Group ta masu daraja, sun yi zama da shugaban kasa.

Bola Ahmed Tinubu ya yi kus-kus da wadannan ‘yan siyasa ne a lokacin da jaridar Tribune ta ce ana rade-radin za su sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC.

Da yake jawabi a yammacin Alhamis, Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya shaida cewa sun ziyarci Bola Tinubu ne kurum domin sha’anin Najeriya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Muhimman Kalaman da Gwamnonin G5 Suka Faɗa Wa Shugaba Tinubu Sun Bayyana

'Yan G5 na PDP
'Yan G5 tare da Bola Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

A cewar Makinde, ‘yan G5 sun fadawa shugaba Tinubu matsayarsu a kan adalci da zaman lafiya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

'Yan G5 a Aso Villa

Mai girma Gwamnan Oyo ya na tare da sauran mutane hudu wanda yanzu dukkansu sun sauka daga kujerun da suke rike da su na Gwamnonin jihohinsu.

Jagororin na PDP da suka kawo mata matsala a zaben 2023 sun shaidawa ‘yan jarida cewa sha’anin gina kasa yana da wahala, kuma yana bukatar nazari.

Makinde ya nuna cewa ba wannan ne zai zama haduwarsu ta karshe da shugaban kasar ba, za su cigaba da yin zama domin a bullowa hanyar yin gyara.

Jawabin Seyi Makinde

"Gina kasa yana da matukar wahala. Dole ka rika bibiya a ko yaushe, domin sanin halin da ake ciki, da kuma inda aka dosa.
Saboda haka kun gane, dole mu cigaba da haduwa da shugaban kasa, domin kuwa mu sanar da shi abubuwan da suke faruwa.

Kara karanta wannan

Shugabancin Majalisa: Wasu ‘Yan G7 Sun Ki Zuwa Taron da Bola Tinubu Ya Kira

‘Yan G5 na kungiyar Integrity ta zo ne domin sanar da shugaban kasa abin da aka san ta a kai na adalci, gaskiya da daidaito."

- Seyi Makinde

Legit.ng Hausa ba ta da labarin Tinubu ya yi magana a kan dalilinsa na haduwa da jiga-jigan jam’iyyar adawar, illa iyaka ya nuna hotunan zaman na su a jiya.

Rusau a Kano

Alamu na kara nuna cewa duk wasu masu gini a filayen gwamnati, masallatai, maƙabarta, makarantu, asibitoci da gefen badala sun shiga uku a jihar Kano.

An ji labari sabon Gwamnan Kano da aka fi sani da Abba Gida Gida ya yi umarnin rusa gine-ginen da aka yi a filayen da mallakin gwamnati ne ko na al’umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel