Majalisa Ta 10: Mambobi 67 Na Bayan Yari, Abdul Ningi Ya Ce Dole a Bar ’Yan Majalisa Su Zabi Son Ransu

Majalisa Ta 10: Mambobi 67 Na Bayan Yari, Abdul Ningi Ya Ce Dole a Bar ’Yan Majalisa Su Zabi Son Ransu

  • Sanata Abdul Ningi ya bayyana cewa Abdulaziz Yari ya na da mambobi akalla 67 da suke goyon bayansa
  • Ningi ya bayyana haka ne yayin taron ganawa da ‘yan jaridu a ranar Laraba 6 ga watan Yuni a Abuja
  • Abdulaziz Yari na daga cikin sanatocin da suka nuna sha’awarsu ta tsayawa takarar majalisar ta 10

FCT, Abuja – Tsohon mataimakin masu rinjaye a majalisar dattawa ta bakwai, Abdul Ningi ya ce akalla sanatoci 67 ne ke mara wa Abdulaziz Yari baya a neman takarar shugabancin majalisar.

Ningi ya bayyana haka ne yayin taron ganawa da ‘yan jaridu, ya ce lokaci ya yi da za a bari ‘yan majalisa su zabi shugabanninsu.

Abdul Ningi ya goyi bayan Yari, ya ce mambobi 67 suna tare da su
Abdul Ningi Ya Ce Dole a Bar ’Yan Majalisa Su Zabi Son Ransu. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Yari wanda yake wakiltar Zamfara ta Yamma kuma tsohon gwamnan jihar ya na daga cikin wadanda suka nuna sha’awar tsayawa takarar kujerar majalisar.

Kara karanta wannan

An Gagara Shawo Kan Tsohon Gwamnan APC, Ya Dage da Neman Shugabancin Majalisa

Jam'iyyar APC ta zabi Akpabio a matsayin wanda zai gaji kujerar

Jam’iyya mai mulki ta APC ta zabi Godswill Akpabio a matsayin wanda zai gaji shugabancin kujerar majalisar, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Ningi:

“Lissafinmu na baya-bayan nan, ya nuna cewa a jiya Talata 6 ga watan Mayu, mambobi na kara nuna goyon bayansu.
“Ni ba dan jam’iayyar APC ba ne, ban san yadda kwamitin tsare-tsarensu ya ke ba, amma shekaru 20 kenan ana samun matsala saboda kakaba wa ‘yan majalisa shugabanni tun lokacin Enwerem da Chuba.
“Ya kamata a bari mambobi su zabi wandanda suke so a ra’ayi na, jam’iyyar PDP sun yi kuskure makamancin wannan, ya kamata APC su guji aikata haka, kamar yadda jam’iyyar ta zabi shugabanta haka ya kamata majalisar ma su zabi shugabanninsu.

Ya bayyana irin kwarewar da Yari ke da shi na shugabanci

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Mambobi Majalisa Sun Zabi Kakakin Majalisar Dokoki Jihar APC Karo Na 3 a Jere

Ya kara da cewa Abdulaziz Yari yana da kwarewar da ya dace da zama shugaban majalisar.

Sanatan ya kara da cewa:

“Tabbas, Yari yana da kwarewar da zai rike shugabancin majalisa, shi yasa muke goyon bayansa, muma mun rike mukamai a majalisar ba wai ‘yan kallo kadai ba ne, ana bukatar irinmu don aiwatar da abin da ake bukata, goyon bayan Yari ba maganan kudi ba ce.”

Majalisa Ta 10: ‘Ba Na Sha’awar Neman Kujerar Majalisa’, Cewar Ahmad Lawan

A wani labarin, Sanata Ahmed Lawan ya bayyana cewa bai ta ba nuna sha'awar neman kujerar majalisar ta 10 ba.

Lawan ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da Shugaba Tinubu a Abuja a ranar Alhamis 1 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel