An Ba Wa Hammata Iska Tsakanin Sojoji Da Matasa A Fitacciyar Jihar Arewa, Mutane 2 Suka Rasa Ransu

An Ba Wa Hammata Iska Tsakanin Sojoji Da Matasa A Fitacciyar Jihar Arewa, Mutane 2 Suka Rasa Ransu

  • An samu hargitsi tsakanin jami’an sojoji da kuma wasu matasa a garin Jos ta Kudu, da ke jihar Plateau
  • Lamarin ya faru ne a Maraban Jema’a, yayin da mutane biyu suka rasa rayukansu da kuma raunata wasu
  • Hargitisin ya faru ne a ranar Lititnin 5 ga watan Yuni wanda lamarin ya ta da hankulan jama’a

Jihar Plateau – Mutane biyu sun mutu yayin da wasu suka jikkata a lokacin da yamutsi ya barke tsakanin wasu matasa da jami’an sojoji a jihar Plateau.

Hargitsin ya faru ne a Maraban Jema’a a karamar hukumar Jos ta Kudu tsakanin jami’an sojoji da matasa.

Jihar Plateau
An Bai Wa Hammata Iska Tsakanin Sojoji da Matasa, Yayin da Mutane Biyu Suka Rasa Ransu. Hoto: Daily Post.
Asali: UGC

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin 5 ga watan Yuni wanda ya ta da hankulan jama’a a yankin.

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya sa hanyar Maraban Jema’a zuwa Zerwan Junction da ta nufi cikin garin Jos babu motoci da mutane akan titi saboda tsohon rikici.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda farkon rikicin ya fara

Hargitsin ya fara ne lokacin da wasu mutane da suke dawo wa daga asibiti zuwa makabarta don binne gawa, suka isa wurin da ake binciken ababan hawa.

Punch ta tabbatar cewa masu makokin wadanda yawancinsu matasa ne suna kan babura lokacin da suka isa wurin binciken ababan hawan, sai jami’an sojojin suka bukace su da su sauko su tura ababan hawan nasu kamar yadda aka saba.

Matasan sun ki bin umarnin sojojin

Sai matasan suka ki bin umarnin sojojin, sai suka yi kokarin rokon sojojin don su taimaka musu su wuce.

Daga bisani dukkan bangarorin biyu ba su samu fahimtar juna ba, wanda hakan ya jawo harbe-harbe.

Wata majiya ta tabbatar da harbin matasa uku a yayin rikicin.

A cewar majiyar:

“Mutum daya ya mutu nan take, yayin da aka tafi da daya zuwa asibiti kafin shima ya ce ga garinku.”

Majiyar ta kara da cewa matasan nan take suka fusata yayin da suka cinnawa motar sojojin wuta tare da yin zanga-zanga.

Kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ Kyaftin John James bai ce komai game da faruwar lamarin ba, yayin aka kira shi da tura masa sakon karta kwana.

Jami'an Jami'an Tsaro Sun Mamaye Majalisar Dokokin Jihar Filato

A wani labarin, jamia'n tsaro sun mamaye majalisar dokokin jihar Plateau da ke Arewa ta Tsakiya.

Hakan ya biyon bayan rikici da ake ta samu a majalisar tun bayan da dakarun rundunar 'yan sandan jihar suka mamaye zauren majalisar da kuma kwace ikon majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel