Karshen Alewa: ’Yan Sanda Sun Ragargaji ’Yan Bindiga, Sun Ceto Yara 9 da Suka Sace

Karshen Alewa: ’Yan Sanda Sun Ragargaji ’Yan Bindiga, Sun Ceto Yara 9 da Suka Sace

  • Jami’an ‘yan sandan jihar Zamfara sun yi nasarar kubutar da yara tara da ‘yan bindiga suka sace a ranar Asabar 3 ga watan Yuni
  • ‘Yan bindigan sun sace yaran ne a kauyen Gora-Namaye a cikin karamar hukumar Maradun da ke jihar
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar ne ya bayyana haka a wata sanarwa a ranar Lahadi 4 ga watan Yuni

Jihar Zamfara – Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa jami’anta sun yi nasarar kwato yara tara da ‘yan bindiga suka sace.

‘Yan bindiga sun sace yaran ne a kauyen Gora-Namaye a karamar hukumar Maradun da ke jihar.

Jihar Zamfara
Jami’an ’Yan Sanda Sun Yi Nasarar Kubutar da Yara Tara Da ’Yan Bindiga Suka Sace. Hoto: Daily Post.
Asali: UGC

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar ne ya bayyana haka a wata sanarwa a Gusau babban birnin jihar a ranar Lahadi 4 ga watan Yuni, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Tirkashi: ’Yan Sanda Sun Cafke Matar da Ta Damfari Mutane Fiye da 100 Kudi Har N150m

Sanarwar ta bayyana yadda aka sace yaran

A cewarsa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“A ranar 3 ga watan Yuni na wannan shekara da misalin karfe 8:14 na dare, mun samu rahoto daga Dagacin kauyen Gora-Namaye a karamar hukumar Maradun cewa an sace yara tara da suka hada da maza da mata.
“’Yan bindigan sun sace yaran ne lokacin da iyayensu suka tura su zuwa dauko itacen girki a cikin daji don amfani da shi a gida.
“A lokacin da muka samu wannan rahoto, hadakar jami’an tsaro sun isa wurin da gaggawa don ceto yaran, yayin da daga bisani aka yi nasarar kwato yaran."

'Yan sandan sun mika yaran ga iyayensu

Kakakin ya kara da cewa, jami’ansu sun riga sun dauki yaran zuwa gidan iyayensu don samun kwanciyar hankali, cewar TheCable.

Ya kara da cewa:

“Muna iya kokarin mu don ganin mun zakulo ‘yan ta’addan don su fiskanci hukuncin hukuma daidai da abin da suka aikata."

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Afkawa Mutane Yayin Jana'iza A Sokoto, Sun Bindige Da Dama

Idan ba a manta ba a ranar Asabar ne 3 ga watan Yuni, ‘yan bindiga suka kai hari kauyukan karamar hukumar Maradun da ke jihar tare da hallaka mutane da dama.

Yan Bindiga Sun Sheke Mutane 10 a Zamfara, Gwamna Ya Yi Alkawarin Kawo Karshen Rashin Tsaro

A wani labarin, Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara sun tabbatar da kisan mutane goma a kauyuka da dama na jihar.

'Yan bindigan sun kai harin ne a kauyen Sakiddar Magaji da Jankobo a karamar hukumar Maradun da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel