Yan Bindiga Sun Afkawa Mutane Yayin Jana'iza A Sokoto, Sun Bindige Da Dama

Yan Bindiga Sun Afkawa Mutane Yayin Jana'iza A Sokoto, Sun Bindige Da Dama

  • ‘Yan bindiga sun kai hari a kauyukan jihar Sokoto tare da kashe mutane 37 da raunata da dama a harin a ranar Asabar
  • Hare-haren ya afku ne a kauyukan Raka da Raka Dutse da kuma Filin Gawa a karamar hukumar Tangaza da ke jihar
  • Tsohon shugaban yankin, Bashar Kalenjeni ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce har yanzu ba a binne gawarwakin ba

Jihar Sokoto – Akalla mutane fiye da 37 ne suka mutu yayin da da dama suka samu raunuka a wani harin ‘yan bindiga a jihar Sokoto.

An kai hare-haren ne a yankuna da dama a karamar hukumar Tangaza da ke jihar a ranar Asabar 3 ga watan Yuni.

Hare-haren jihar Sokoto
Yan Bindiga Sun Far Wa Wasu Kauyuka, Tare da Kashe Mutane Da Dama. Hoto: Within Nigeria.
Asali: Facebook

Kauyukan sun hada da Raka da Raka Dutse da kuma Filin Gawa, kamar yadda shaidun gani da ido suka tabbatar wa jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Yan Bindiga Sun Sheke Mutane 10 a Zamfara, Gwamna Ya Yi Allah Wadai Da Harin

Tsohon shugaban yankin ya tabbatar da faruwar lamarin

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, tsohon shugaban wannan yanki, Bashar Kalenjeni ya ce mutane 18 ne suka mutu a kauyen Raka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahotanni sun kuma ce an kashe mutane 17 a kauyen Raka Dutse da Filin Gawa a dalilin hare-haren.

A cewarsa:

“Mun yi shirin binne gawarwakin da dare amma sai ‘yan bindigan suka sake dawo wa suka tarwatsa mu, har zuwa safiyar yau Lahadi ba a binne gawarwakin ba suna can a zube.
"Ya ce laifin ‘yan kauyen kawai shi ne saboda sun ki biyan kudin haraji da ‘yan bindigan suka kakaba musu.
“Yan bindigan sun kakaba mana biyan haraji a yankunan nan, wanda suke son ya fara aiki nan take, da kuma juya ‘yan yankin yadda suke so."

Ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Kan Al'umma a Arewa, Sun Kashe Mutane Masu Yawan Gaske

“Amma ‘yan kauyen sun ki biyan harajin, saboda haka suka kawo hari tare da kashe mutane 37 da raunata mutane da dama wanda yanzu haka suna babban asibitin Gwadabawa don samun kulawa.
“Akwai mutane da dama wadanda ba a san inda suke ba, inda ya ce a yanzu haka muna jiran jami’an tsaro su kaimu mu binne gawarwakin.

'Yan sanda ba su san da labarin kai harin ba

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, ASP Ahmad Rufa’i ya ce ba shi da masaniya akan wadannan hare-hare.

Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 10 a Zamfara, Gwamna Ya Yi Allah Wadai Da Harin 'Yan Bindigan

A wani labarin, akalla mutane 10 suka rasa rayukansu yayin da da dama suka samu raunuka a wani sabon hari da 'yan bindiga suka kai a jihar Zamfara.

Yayin da yake nuna alhininsa, Gwaman jihar, Dauda Lawal ya yi alkawarin kawo karshen rashin tsaro a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel