Abubuwa 5 Da ’Yan Najeriya Ya Kamata Su Sani Game Da Cire Tallafin Mai

Abubuwa 5 Da ’Yan Najeriya Ya Kamata Su Sani Game Da Cire Tallafin Mai

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayu bayan da aka rantsar da shi a Abuja
  • Cire tallafin ya jawo cece-kuce a kasar yayin da mutane da dama ke ganin cire tallafin a wannan lokaci kuskure ne
  • Hakan ya jawo wahalhalu ga ‘yan kasar, musamman yadda a farko a ka fara samun cinkoso a gidajen mai ga kuma tsada

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu a yayin bikin rantsar da shi ya bayyana cire tallafin man fetur.

Bayan sanar da cire tallafin, farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi inda wasu gidajen mai suke siyar da litan mai har N700 kafin daga bisani a wasu wurare aka fara siyar da litan N550.

Layin mai a Najeriya
Abubuwa 5 Da ’Yan Najeriya Ya Kamata Su Sani Game da Cire Tallafin Mai da Shugaba Tinubu Ya Yi. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Ana ta hasashen cewa kamfanin man fetur na NNPC zai kara farashin man a watan Yuni, amma sai suka kara farashin kwana biyu da sanarwar shugaban kasar, 31 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

To fah: Farashin fetur ya tashi a wata kasa saboda Tinubu ya janye tallafi a Najeriya

Yayin bayyana dalilin karin farashin man fetur din, shugaban kamfanin man fetur na Najeriya, Mele Kyari ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba ta biya kudin tallafin ba a shekarar 2022.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa a watan Maris na shekarar 2023, gwamnatin ta rike wa kamfanin kudaden tallafin man fetur har Naira Tiriliyan 2.3, cewar Punch.

Jerin abubuwa guda biyar muhammai da ya kamata ku sani game da kamfanin NNPC da harkar man fetur a kasuwanni:

1. Duk da cewa kamfanin NNPC tsohon kaya suke siyarwa, amma kamfanin sun ce za su siyar a sabon farashin don samun damar siyo wani mai din.

2. Kamfanin NNPC ba ita kadai za ta kasance mai shigo da man fetur ba zuwa cikin kasar.

3. Kamfanin har ila yau, ba zai iya sauya farashin mai a kasuwan hada-hadar man fetur din ba, kowane dan kasuwa zai iya saka farashin da yake so.

Kara karanta wannan

Tsadar mai: Kungiyar 'yan jarida ta tubure, ta ce za ta yi gagarumar zanga-zanga a Najeriya

4. Sauya farashin mai a kasuwa zai zama karkashin ikon ‘yan kasuwa ne kadai ba kamfanin NNPC ba.

5. Gwamnati, ana ta bangaren za ta tabbatar ba a cutar da ‘yan kasa ba musamman a harkan man fetur.

Kamfanin NNPC har ila yau, ya musanta cewa idan aka fara samar da man a cikin gida, man fetur zai yi araha a kasar, inda ya ce hakan ba abin da zai sauya a farashin.

NNPC Ya Kara Farashin Man Fetur a Duk Gidajen Mai da Ke Karkashinsa

A wani labarin, Kamfanin man fetur, NNPC ya kara farashin man fetur a dukkan gidajen mai da ke karkashinsa.

A wata sanarwa da Garba Deen Muhammad, kakakin kamfanin ya fitar, ya ce karin farashin ya yi daidai da yadda tsarin kasuwa ya ke a yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel