Kungiyar ’Yan Najeriya Ta Fusata da Tinubu, Ta Ce Za Ta Fada Yajin Aiki, Za Ta Yi Kazamar Zanga-Zanga

Kungiyar ’Yan Najeriya Ta Fusata da Tinubu, Ta Ce Za Ta Fada Yajin Aiki, Za Ta Yi Kazamar Zanga-Zanga

  • Kungiyar ‘yan jarida a Najeriya ta tubure, ta ce sam bata amince da karin farashin man fetur da aka yi ba a kasar
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Bola Tinubu ya cire tallafin mai gaba daya a kasar saboda dalilai
  • NLC da NUJ sun tsayar da batun za su fara yajin aiki da zanga-zanga a fadin jihohin kasar nan a ranar Laraba

FCT, Abuja - Yayin da kasa ke ci gaba da shiga tsada, kungiyar ‘yan jarida a Najeriya (NUJ) ta bayyana aniyarta na tsundumawa yajin aiki.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kungiyar kwadago ta Najeriya ta ce za ta tsunduma yajin aiki a ranar Laraba mai zuwa.

Duk wadannan kungiyoyi sun bayyana cewa, za su fara yajin ne biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi a ranar 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aikin Gama Gari, Ta Ba Gwamnatin Tinubu Sabon Wa’adi

NUJ ta ce bata amince da karin farashin mai ba
Tambarin kungiyar 'yan jarida ta Najeriya | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

NLC ta yi daidai, inji kungiyar NUJ

A cewar sanarwar da NUJ ta fitar bayan ganawa da kwamitin gudanarwarta a yau Asabar 3 ga watan Yuni, ta yi tattaunawa kan matsaya game da cire tallafin mai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, ta bayyana goyon bayanta ga tuburewar da kungiyar kwadago ta NLC ta yi tare da bayyana daukar matakin fadawa yajin aiki.

A cewar NUJ, cire tallafin mai fetur a Najeriya ya jefa ‘yan kasar da dama cikin hadari da mawuyacin halin rayuwa wanda ke bukatar matakin gaggawa.

Hakazalika, ta koka ga yadda sauran kayayyaki a kasar ke kara tashin gwauron zabi, inda tace komai na karewa ne kan talakawa, kuma akwai mambobinta a ciki.

A fara yaji da zanga-zanga

A bangare guda, kungiyar ta yi kira ga mambobinta a fadin jihohin Najeriya da su ba da hadin kai tare da fara wannan yajin aikin a ranar 7 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Fara Mulki da Ciwon Kai, ‘Yan Kwadago Sun Sa Ranar Shiga Yajin-Aiki

Haka kuma, ta ce mambobin su fara zanga-zanga a fadin kasar har sai kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya janye karin farashin da ya yi na man fetur, BBC ta tattaro.

Har yanzu ana ci gaba da cece-kuce kan cire tallafin man fetur da sabuwar gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta yi a Najeriya.

Matatar Dangote ba za ta sa farashin mai ya sauka na, inji NNPCL

A wani labarin, kunji yadda kamfanin man fetur na NNPCL ya bayyana hasashe game da makomar farashin man fetur a Najeriya.

Kamfanin ya yi tsokaci da cewa, ba lallai matatar man fetur da Dangote ya gina ta kawo saukin farashin mai a Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel