Ruwan Dare: Yaddajanye Farashin Man Fetur a Najeriya Ya Jawo Tsadar Mai a Jamhuriyar Benin

Ruwan Dare: Yaddajanye Farashin Man Fetur a Najeriya Ya Jawo Tsadar Mai a Jamhuriyar Benin

  • Ta bayyana cewa, gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta fara ne da sanar da janye tallafin man fetur ba tare da shirin ‘yan Najeriya ba
  • Ya zuwa yanzu, karin farashin man fetur da aka yi a Najeriya ya shafi kasar makwabta ta Benin
  • Akwai rahotanni da ke shigo mana cewa, ana kai kayayyakin da suka shafi man fetur zuwa kasar ta Benin a biye ana siyarwa a bakin titi

A bikin rantsar dashi, shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana janye tallafin man fetur a Najeriya a ranar 29 ga watan Mayu.

Sanarwar tasa ta jawo nan take dillalan man fetur a kasar suka gallazawa ‘yan kasa ta hanyar garkame gidajen mai, wasu kuma nan take suka kara farashi.

Sai dai, tasirin janye tallafin ba a Najeriya kadai ya tsaya ba, domin kuwa ya tsallaka har kasar Benin da ke makwabtaka da Najeriya.

Kara karanta wannan

Ba haka ake ba: Atiku ya ankarar da Tinubu kan yadda ake cire tallafin fetur, ya caccaki tsarinsa

Zare tallafin mai a Najeriya da Tinubu ya yi ya shafi jamhriyar Benin
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu na Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Yadda tsadar mai a Najeriya ya shafi Benin

Ya zuwa yanzu, farashin man fetur ya karu a Benin, cikin mako guda da ya karu a Najeriya baya janye tallafin na man fetur a nan gida Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar rahoton BBC Pidgin, farashin mai a Benin ya karu jim kadan bayan da Najeriya ta shiga halin ni ‘yasu da aka janye tallafi.

Farashin man fetur a Benin ya karu daga CFA 450 zuwa CFA 700 har na zuwa CF 800 a wuraren, kamar yadda wani mazaunin kasar, Clement Sodji ya bayyana.

Akwai kuma rahotanni da ke cewa, wasu nau’ikan albarkatun mai da ake samarwa a Najeriya kuma suke dauke da tallafi, ana shigar dasu Benin a boye tare da siyar dasu a ain titi.

An kuma tattaro cewa, albarkatun mai na Najeriya na da tasiri ainun ga kasuwanni a kasashen Yammacin Afrika.

Kara karanta wannan

Tsadar mai: Kungiyar 'yan jarida ta tubure, ta ce za ta yi gagarumar zanga-zanga a Najeriya

Atiku ya caccaki Tinubu kan janye tallafin man fetur

Yayin da Bola Ahmad Tinubu ya kama mulki tare da janyewa ‘yan Najeriya tallafin man fetur, abokin hamayyarsa a zaben 2023, Atiku Abubakar ya magantu kan lamarin.

A cewar Atiku, bai kamata shugaban na Najeriya ya cire tallafi haka kawai baktatan ba tare da la’akari da wasu bangarori daban-daban ba.

Ya kuma tuna masa yadda gwamnatinsu ta PDP ta yi aikin janye tallafin mai a shekarun mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel