Almajiri Ya Gamu Da Ajalinsa Bayan Ya Fada Rafi a Jihar Kano

Almajiri Ya Gamu Da Ajalinsa Bayan Ya Fada Rafi a Jihar Kano

  • Wani almajiri ya gamu da ajalinsa bayan tsautsayi ya sanya ya nutse a cikin wani kududdufi a ƙaramar hukumar Karaye ta Kano
  • Almajirin ya nutse cikin kududdufin ne bayan santsi ya kwashe ya faɗa ciki lokacin ɗa suke wanke jiki a tare da abokansa
  • Jami'an kwana-kwana sun samu nasarar ceto almajiirin wanda daga baga ya ce ga garin ku nan bayan an kai shi asibiti

Jihar Kano - Wani ƙaramin yaro almajiri mai shekara 13 a duniya mai suna suna Yusuf Magaji, ya nutse a cikin rafi a ƙauyen Makugara cikin ƙaramar hukumar Karaye ta jihar Kano, rahoton Vanguard.

Kakakin hukumar ƴan kwana-kwana ta jihar Kano, Saminu Yusuf, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya bayyana cewa santsi ne ya kwashe almajirin ya fada cikin rafin lokacin da suke wanka a bakin rafin tare da sauran abokansa.

Almajiri ya rasu bayan ya nutse cikin rafi a Kano
Masu ceto na ceton wani daga cikin ruwa. (Ba a inda.lamarin ya auku ba) Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Kakakin ya bayyana cewa malamin tsangayar Malam Nafiu Na Adama, shi ne ya yi wa jami'an hukumar kiran gaggawa kan halin da ake ciki.

Yusif ya ce jami'an hukumar na Karaye sun samu nasarar ceto almajirin a galabaice, inda daga bisani likita ya tabbatar da rasuwarsa bayan an kai shi asibiti, rahoton Aminiya ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"A ranar Alhamis da misalin ƙarfe 1:31 na rana mun samu kiran gaggawa a ofishin mu na Karaye daga wajen wani Malam Nafi'u Na Adama, wanda ya sanar da cewa almajirinsa a tsangayarsa ta Makugara ya faɗa rafi."
"A cewarsa almajiran suna kan hanyarsu ta zuwa wani ƙauye ne, suka tsaya a bakin rafin domin wanke jikinsu, amma sai tsautsayi ya sanya santsi ya kwashe shi ya faɗa cikin rafin inda ya yi ƙoƙarin fitowa amma ya kasa."

Almajirin ya rasu daga baya bayan an ceto shi

Kakakin ya bayyana cewa jami'an hukumar na ofishin Karaye sun samu nasarar ceto almajirin wanda ya galabaita, sannan suka tafi da shi zuwa asibitin kwararru na Karaye, inda a can ne likitoci suka tabbatar ya rasu.

Yusuf ya bayyana cewa an miƙa gawar almajirin ga Malam Nafiu Na Adama, shugaban tsangayar domin yi masa jana'iza.

Malamin Jami'a Ya Rasu Yana Cikin Barci

A wani rahoton na daban kuma, wani malamin jami'a a jihar Kwara ya riga mu gidan gaskiya yana cikin barcinsa.

Dakta Ajeibe Issa na jami'ar jihar Kwara da ke Malete, ya gamu da ajalinsa a gidansa da ke birnin Ilorin, babban birnin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel