Iyaye Sun Bayyana Yadda Wasu ’Yan Banga Suka Lakadawa Dansu Duka Har Lahira a Kano

Iyaye Sun Bayyana Yadda Wasu ’Yan Banga Suka Lakadawa Dansu Duka Har Lahira a Kano

  • Mahaifin yaron Alhaji Muhammad Kwabe ya ce 'yan banga sun lakaɗawa dansa dukan tsiya a lokacin da aka aikesa da safiyar ranar Litinin
  • Ya kuma ce 'yan bangar sun hana a kai shi asibiti a lokacin da lamarin ya faru har sai bayan da lokaci ya ƙure
  • Kakan matashin ya nemi mai martaba Sarkin Kano da ya sa a bi masa haƙƙin ɗansa saboda a cewarsa ba a samesa da laifin komai ba

Kano - Iyayen wani matashi mai suna Abdurrazak Kabiru Kwabe, ɗan shekara 22, sun zargi wasu ‘yan banga na Hausawa a jihar Kano da lakaɗawa dansu duka har lahira.

Marigayin ya kasance kafin rasuwarsa yana sana'ar kafinta ne a cikin Kano, jaridar Daily Trust ta kawo rahoto.

Yan banga sun lakadawa matashi duka har lahira a Kano
Iyaye sun zargi 'yan banga da lakadawa dansu duka har lahira a Kano. Hoto: Kano Focus
Asali: UGC

An aikesa ne lokacin da abin ya faru

Mahaifinsa, Alhaji Muhammad Adamu Kwabe, ya ce an kashe marigayin ne lokacin da aka aike shi da safiyar ranar Litinin ɗin nan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yace:

“Ina gida ne ɗaya daga cikin ‘yan uwana ya kira ni na zo na ga yadda ’yan banga suka yi wa Abdulrazak Kabiru dukan tsiya. Na ga jini na kwararowa daga kansa. Na yi kokarin tambayarsu game da laifin da ya aikata. Sai kawai suka tafi da shi cikin motarsu. Wani kawunsa ne ya bi su ya roke su kan su bari a kai shi asibiti amma suka ƙi.
“Daga baya ne suka yanke shawarar kawo mana shi gida. Daga nan muka kai shi asibitin Sheka, sai suka tura mu sashin gaggawa na asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad.”
"Ba a sami ɗana da wani laifi ba, ba su same shi da komai ba don me 'yan banga za su kashe shi?"

Iyayen sun nemi a bi wa ɗan nasu haƙƙinsa

Kakan matashin ya roƙi Sarkin Kano da ya tabbatar da an bi wa jikansa hakkinsa, saboda a cewarsa, ’yan bangan sun kashe shi ne bisa zalunci.

Kwamandan ‘yan banga na jihar Kano, Shehu Kabiru, ya ce tuni aka kafa kwamitin da zai binciki lamarin.

Da aka tuntuɓi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar (PPRO), SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ya samu labarin lamarin kuma ya yi alkawarin zai bayar da bayani daga baya.

Yan sanda sun kashe ƙasurguman 'yan bindiga a Katsina

A wani labarin na daban kuma, rundunar 'yan sanda a jihar Katsina, ta tabbatar da nasarar da jami'anta suka yi na kashe wasu ƙasurguman 'yan bindiga guda biyu a lokacin da suka kai hari a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Bindawa a jihar.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Katsina Abubakar Sadiq Aliyu ne ya bayyana hakan, inda ya ce jami'ansu sun kuma yi nasarar ƙwatar wasu makamai daga hannun 'yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel