Bola Tinubu: Abubuwa 2 Da Ke Faruwa a Kasa Wadanda Tinubu Bai Yi Magana a Kansu Ba Ranar Da Aka Rantsar Da Shi

Bola Tinubu: Abubuwa 2 Da Ke Faruwa a Kasa Wadanda Tinubu Bai Yi Magana a Kansu Ba Ranar Da Aka Rantsar Da Shi

  • A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu ne Bola Tinubu ya karbi ragamar shugabancin Najeriya daga hannun tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari
  • A cikin jawaban da Tinubu ya gabatar, bai yi magana kan yajin aikin ASUU ba, wanda hakan ya sa ake fargabar komawa gidan jiya
  • Haka nan Tinubu bai yi magana kan yajin aikin likitoci ba, da kuma ƙalubalen da ake fuskanta a fannin kiwon lafiya a jawaban nasa

Shugaban kasa Bola Tinubu, ya sha faɗa tun lokacin yaƙin neman zaɓe cewa shi fa da aiki zai zo, ba da wasa ba, saboda haka jama'a sun fara shaida hakan tun lokacin da ya karɓi mulki.

A ranar da Tinubu ya karɓi mulki ne ya sanar da cire tallafin man fetur, wanda ya ce babu wani tanadi da aka yi masa cikin kasafin kuɗin shekarar 2023 da tsohuwar gwamnati ta Buhari.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Ba Hafsoshin Tsaro Sabon Salon Yaki da Rashin Tsaro a Najeriya

Tinubu bai ce komai ba kan yajin aikin ASUU da na Likitoci
Shugaba Tinubu bai yi magana kan batun yajin aikin ASUU da na Likitoci ba. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Waɗannan kalamai nasa ne suka sanya ‘yan kasuwar man fetur, fara ɗaukar mataki na ƙara farashin man tun kafin ma Tinubun ya sauka daga kan dandamalin taron.

Duk da wasu masana harkokin siyasa sun yaba masa kan jawaban da ya yi a wajen bikin rantsuwar, har yanzu akwai wasu muhimman batutuwa guda 2 da ke ci gaba da wakana a ƙasar waɗanda Tinubu bai sanyosu cikin jawaban ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Waɗannan batutuwa 2 kuma na daga cikin abubuwa masu muhimmanci da suke damun 'yan Najeriya. Batutuwan sune, yajin aikin ASUU da na Likitoci.

Yajin aikin ASUU

Yajin aikin ASUU batu ne da tuntuni ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. A cikin jawaban da Tinubu ya yi wajen bikin rantsar da shi, bai yi magana akan yajin aikin da malaman jami'o'i (ASUU) ke yawan yi ba.

Kara karanta wannan

Manajan NNPC, Mele Kyari Ya Yi Bayani Dangane Da Farashin Da Ake Siyan Man Fetur Yanzu a Kasuwa

Ko a gwamnatin da ta gabata, tilastawa ƙungiyar aka yi wajen kawo ƙarshen yajin aikin da ta daɗe tana yi, ta hanyar kotun masana’antu.

ASUU ta janye yajin aikin bayan hakan, ba tare da samun biyan buƙatun da ta zo da su ba, ana gudun kada Tinubu ya ɗora kan irin hakan kamar yadda Buhari ya yi a lokacinsa.

Yajin aikin likitoci

Wani muhimmin lamari da ke yawan faruwa a Najeriya shi ne yajin aikin likitoci, wanda shi ma Tinubu bai ce komai a kansa ba wajen bikin rantsar da shi.

Kungiyar Likitoci ta kasa (NARD) ta janye yajin aikin kwanaki 7 kafin bikin rantsar da Tinubu bayan sanya hannu kan wata yarjejeniyar da gwamnatin da ta gabata.

A yanzu haka dai akwai ƙungiyar hadin guiwa ta ma'aikatan lafiya (JOHESU) da ta shiga yajin aiki tun ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu, kwanaki 5 gabanin rantsar da Tinubu. Sai dai kuma sabon shugaban bai yi wani bayani ba kan yadda za a magance matsalar ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu Na Shirin Rage Alawus Din Yan Bautar Kasa? Gaskiya Ta Bayyana

NNPC na bin Gwamnatin Tarayya bashi, cewar Mele Kyari

A labarinmu na baya kun jiyo manajan daraktan kamfanin mai na ƙasa (NNPC), Mele Kyari na bayyana cewa gwamnati ba za ta iya ci gaba da biyan kuɗaɗen tallafin man fetur ba.

Mele Kyari ya ce a yanzu haka NNPC na bin gwamnati bashin kuɗaɗe masu yawan gaske, wanda dalilin haka dole ne ma gwamnatin ta cire tallafin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel