Sarki Aminu Ado Bayero Ya Aika Bukata a Wajen Tinubu Kafin Ya Shiga Aso Rock

Sarki Aminu Ado Bayero Ya Aika Bukata a Wajen Tinubu Kafin Ya Shiga Aso Rock

  • Aminu Ado Bayero ya halarci taro da aka shirya domin zaman lafiya tsakanin addinai a Kano
  • Sarkin Kano ya ce ana bukatar a kafa ma’aikata ta musamman ta tarayya domin sha’anin addinai
  • A ra’ayin Mai martaba, irin wannan ma’aikata za ta sa al’ummar kasar nan su zauna lafiya da juna

Abuja - Mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya yi kira ga Asiwaju Bola Tinubu a matsayinsa na zababbe kuma shugaba mai jiran gado.

Vanguard ta kawo rahoto a yammacin Juma’a cewa Alhaji Aminu Ado Bayero ya na so a kafa ma’aikata da za ta rika kula da harkokin addini a kasa.

Mai martaba Sarkin Kano ya na ganin hakan zai taimaka sosai a wajen kawo hadin-kai da kwanciyar hankali tsakanain Mabiya addinai da ake da su.

Kara karanta wannan

Dalilai 6 Da Za Su Wargaza Hukuncin Kotun Kano Na Soke Takarar Alex Otti, Fitaccen Lauya Ya Magantu

Sarki Aminu Ado Bayero
Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da Bola Tinubu Hoto: newsday.com.ng
Asali: UGC

Mai martaba Aminu Ado Bayero ya yi wannan kira ne a wajen kaddamar da wani taro na masu aikin hada-kan addinai da ActionAid Nigeria ta shirya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakimin Nasarawa, Babba Dan-Agundi ya wakilci Mai martaba Sarki a wajen zaman da aka yi.

Da yake magana, Babba Dan-Agundi ya ce idan an kafa ma’aikatar addinin, za ta maida hankali sosai wajen koyar da hakuri tsakanin mabanbanta addinai.

Haka zalika Hakimin ya ce ma’aikatar za ta bada karfi wajen ganin an samu fahimtar juna.

Kano garin zaman lafiya

People Gazette ta ce Aminu Bayero ya bayyana Kano a matsayin kasar zaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma lumuna tsakanin addinai dabam-dabam.

Sarkin ya ce akwai matukar bukatar a samu zaman lafiya don haka ake da bukatar ayi duk abin da za a iya domin ganin ‘Yan Adam sun zana lafiya a ban kasa.

Kara karanta wannan

Gaskiyar Bayanan Zaman Kwankwaso, Tinubu, da Sanusi a Faransa Sun Fara Bullowa

Shugaban ActionAid Nigeria a Najeriya, Ene Obi ta yi jawabi a wajen, tana mai nuna muhimmancin addinai, kabilu da mabiya siyasa su hada-kai.

Ganin yadda zafin kishin addini yake jawo ta’adi a Duniya, Dr Muhammad Mustapha-Yahaya ya ce ya dace a tabbatar abin bai shafi mutanen Kano ba.

Nadin Dr. Oluwatoyin Sakirat Madein

Ku na da labari Dr. Oluwatoyin Sakirat Madein za ta zama AGF a sakamakon dakatar da Ahmed Idris, Dr Folashade Yemi-Esan ta sanar da haka a yau.

Sabuwar AGF din ta na da Difloma, PGD, MBA da PhD da shaidar ICAN da ACCA (UK). Duk wani Akanta Janar da aka taba yi a tarihin Najeriya, namiji ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel