Wasu Bayanai 10 a Game da Macen Farko da Ta Hau Kujerar Akanta Janar a Tarihi

Wasu Bayanai 10 a Game da Macen Farko da Ta Hau Kujerar Akanta Janar a Tarihi

  • Mai girma Muhammadu Buhari ya amince Dr. Oluwatoyin Sakirat Madein ta zama sabuwar AGF a kasa
  • Sabuwar Akanta Janar ta kasar ta canji Ahmad Idris wanda aka dakatar saboda zargin rashin gaskiya
  • A tarihi ba a taba samun mace ta rike wannan kujerar ba sai a kan Oluwatoyin Sakirat Madein a 2023

A wani rahoto da aka fitar, Daily Trust ta kawo takaitaccen bayani game da Dr. Oluwatoyin Sakirat Madein.

Ilmi

1. Oluwatoyin Madein ta yi Difloma ne a ilmin Akantanci a 1988 a makarantar koyon aiki ta Moshood Abiola da ke Abeokuta.

2. Daga nan Akantar ta samu Diflomar bayan Digiri (PGD) da Digirgir a harkar kasuwanci (MBA) a jami’ar Olabisi Onabanjo a Ago Iwoye.

3. A 2019, jami’ar Commonwealth ta ba Akantar Digirin girmamawa bangaren ilmin kasuwanci.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Amince da Rabon Sababbin Mukamai a Hukumar FERMA

Shugaban kasa
Shugaban kasa a ofis Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

4. Sabuwar Akanta Janar din ta na da shaidar zama ‘yar kungiyar ACCA ta Ingila da shaidar ICAN.

5. A shekarar 2020, Oluwatoyin Madein ta tafi jami’ar Walden da ke garin Minnesota a Amurka tayi PhD a fannin kula da tattalin arziki.

Sanin aiki

6. Dr. Madein ta shafe tsawon sama da shekaru 30 a matsayin Akanta, mai binciken kudi kuma mai kula da sha’anin tattalin arziki.

7. A hukumar RMRDC aka fara daukar ta aiki, daga nan ta zama cikin ma’aikatan farko da aka dauka a hukumar FEAP da NAPEP.

8. Wannan kwararriyar ma’aikaciya ta rike babbar Jami’ar sashen Akanta a ma’aikatar OPIC da ke Abeokuta kafin ta koma aiki a Abuja.

9. Daga baya tayi aiki a ma’aikatun harkar ‘yan sanda, kasuwanci, ayyuka da gidaje da kuma ma’aikatar matasa da kula da wasanni.

Iyali

10. A karshe Oluwatoyin Madein ta na auren Adeleke Olusina Madein, su na da ‘ya ‘ya hudu.

Kara karanta wannan

Jerin Taro, Wasanni da Shagulgulan Mika Mulki 12 da Za a Shirya na Tsawon Kwana 7

Mukamai a FERMA

A rahoton da mu ka fitar, an ji Femi Adesina ya fitar da jawabi game da wasu nadin mukamai da shugaban kasa ya yi a makon nan.

Muhammadu Buhari ya amince tsawaita wa’adin masu sa ido a kan aikin FERMA, sannan James Akintola ya canji Tunde Lemo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng