Na Gaji: Matar Aure Za Ta Dawo da Sadakin N80k a Gaban Kotu Don a Tsinke Igiyar Aurenta

Na Gaji: Matar Aure Za Ta Dawo da Sadakin N80k a Gaban Kotu Don a Tsinke Igiyar Aurenta

  • Kotun shari’ar Musulunci a Kaduna ta umarci wata mata da ta biya sadakin da aka ba ta na N80,000 a auren
  • Mai shari’a Mallam Muhammad Adamu-Shehu shi ya ba da wannan umarni bayan da matar ta bukaci saki
  • Matar ta tabbatar wa da kotu cewa ta gaji da zaman auren kuma bata bukatar kowace irin sulhu da za a yi

Jihar Kaduna – Wata kotun shari’ar Musulunci da ke Kaduna ta umarci wata mata mai suna Fatima Muhammad da ta dawo da sadakin da ta karba na N80,000, a madadin sakin da ta bukata.

Mai shari’a Mallam Muhammad Adamu-Shehu ne ya ba da wannan umarni bayan matar ta tabbatar da cewa ta gaji da zaman auren da take yi da mijinta, inda ta kara da cewa kuma a shirye take ta dawo da sadakin da ake magana.

Kara karanta wannan

Abin Takaici: Mata Ta Dawo Da Ciki Bayan Zuwa Wurin Alkali Don Ya Raba Auren

sharia
Kotun Musulunci, Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Alkalin kotun har ila yau ya shawarce ta da ta shigar da wata karar don samun daman rike ‘yarsu mai shekaru uku, cewar jaridar Vanguard.

Matar ta fadi matsalarta

Tun farko, matar ta fadawa kotu cewar kwata-kwata auren ya fita akanta, don ba ta bukatar kowace irin sulhu da za a yi a tsakaninsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamanta:

“Na gaji da wannan auren kuma bazan taba zama mai biyayya a gareshi ba, ina rokon kotu da ta bani daman rike ‘yar da muka haifa mai shekaru uku."

Wanda ake karan ta bakin lauyansa Mista L. R. Ibrahim ya shaidawa kotu cewar har yanzu yana kaunar matarsa kuma zai ci gaba da rike ta tsakani da Allah, kamar yadda ya saba a baya a zamansu.

Rahotanni sun ce mijin ya roki kotun da ta bashi isasshen lokaci don ya yi kokarin sasantawa da matar tasa a gida, ba tare da sunzo kotun ba.

Kara karanta wannan

Mata Ta Sumar Da Mijinta Bayan Ta Lakada Masa Duka a Jihar Lagos

Hisbah a jihar Kano Ta Gargadi 'Yan Adaidaita Sahu Kan Manna Hotunan Batsa

A wani labarin, Hukumar Hisbah a jihar Kano ta gargadi masu adaidaita sahu da su guji manna hotunan batsa da sauran abubawa dake bata tarbiya a jihar.

Wannan gargadi ta fitowa ne daga bakin kwamandan hukumar ta jihar, Sheikh Harun Ibn Sina a ofishinsa, inda ya ce aikata irin wadannan ayyuka sun sabawa tsarin addinin Musulunci da koyarwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel